Connect with us

LABARAI

‘Muna Zargin Za A Shiryawa Masu Sauya Sheka Bita-da-kulli

Published

on


Jam’iyyar PDP, tana zargin Jam’iyyar APC da wani shiri na kirkiran kashin kaji ga ‘ya’yanta da suka fice daga cikinta.

Jam’iyyar adawan, wacce ke cewa, a yanzun haka Jam’iyyar ta APC ta shiga cikin rudu kafin babban zaben 2019, ta ce, Jam’iyyar ta APC ta damu tare da firgita kan yadda Jam’iyyar ta PDP ke ta kara samun karbuwa da kuma tururuwan ‘yan Nijeriya daga Jam’iyyu daban-daban zuwa cikinta.

Cikin wata sanarwa da kakakin ta na kasa, Kola Ologbondiyan, ya fitar, PDP din na cewa, “Faruwan hakan ne ya sanya ba mu yi mamakin yadda Jam’iyyar ta APC cikin damuwa da firgita, ke ta daukan nauyin wasu karairayi da yaudaran da ake ta yada su a kan Jam’iyyar ta PDP ba.

“Tun daga dimbin nasarorin da kwamitin da Liyel Imoke, ya shugabanta ya samu na sasantawa da kuma maido da ‘ya’yan Jam’iyyar gida, da kuma yadda kwamitin ya yi kokarin shawo kan ma sauran ‘ya’yan Jam’iyyu zuwa cikin Jam’iyyar ta PDP, hatta ma wadanda suka gano gaskiyan lamarin daga cikin Jam’iyyar ta APC wacce ta rasa makoma ne, Jam’iyyar ta APC hankalinta ya tashi.

 

“Sannan yadda muka yi ta tarban masu kwararowan cikinmu, da irin yarjejinoyin da muka kulla da su gami da hadin kan da ke cikin Jam’iyyar a tsakanin sabbi da ‘ya’yan Jam’iyyar na asali a dukkanin Jihohi, musamman ma a Jihohin Sakkwato, Kogi, Kwara da Jihar Kano, inda daga tsaffi har sabbin masu shigowa aka yi ta shirya masu kasaitattun tarukan tarba.

“Muna sane da cewa, duk abin da Jam’iyyar APC za ta yi domin ganin ta kawo mana rudami cikin yaudara za ta iya yi, har ma da fadin wai akwai sabani a inda babu ma sabanin.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai