Connect with us

LABARAI

Miyetti Allah Ta Yi Tir Da Kisan Fulani Matafiya A Adamawa Da Taraba

Published

on


Kungiyar al’umman fulani makiyaya ta kasa (Miyetti-Allah Cattle Breeders Association), ta yi zargin mahara sun kashe wasu fulani matafiya hudu, ta hanyar sauke su a mota kan hanyar Numan-Demsa, aka kashesu.

Kungiyar Miyetti Allah ta shaidawa manema labarai hakan ne a garin Yola, inda ta ce wasu manoma ne daga yankin kananan hukumomin biyu, ta ke zargin sun yiwa fulanin kisan gilla.

Alhaji Abdu Isa Jaoji, ya ci gaba da cewa akwai wasu Fulani makiyaya uku da’aka saukesu a motar da suke aka kashe aka kuma konesu kurmus, a yankin Guyuk da Shelleng, haka kuma ta zargi matasan Bachama da kisan fulanin a yankunan Bali, Yandan, da wasu mutanen da dama a yankin Mayo-Lope cikin jihar Taraba.

“babbar hanyar Numan-Mayo-Lope, maharan kabilar Bachama sun dakatar da zirga-zirga a kanshi, ana sauke Fulani a mota akashesu, hari ne kawai da’aka kaddamar dashi akan Fulani, yanzu sun fadada shi ga musulmi, saboda haka muna kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su dauki matakan kare rayukan jama’a” inji Jaoji.

“ina da tabbacin an kashe mutane hudu a yankunan kananan hukumomin Numan da Demsa cikin kasa da wata guda, tun lokacin bukin salla ‘yan bindigar Bali, Bachama da Yandan, suke kai hare kan fasinjoji da sauran jama’a a yankin” ya jaddada.

Shima dai shugaban rundunar soja ta 23 dake Yola, Muhammad Bello, ta tabbatar da kashe-kashen da’ake yiwa jama’a matafiya a yankin, sai dai ya ce bashi da masaniyar zargin kaddamar da hari kan jama’a cikin kwanakinnan a yankin.

Bello, ya baiwa matafi da jama’ar yankin tabbacin tsaro ya ce rundunar ta kara yawan jami’an sojoji domin dakile duk wani hari, da kawo karshen ayyukan masu haifar da fitina a yankin bakidaya.

Ya ce ‘yan kasa da fulani makiyaya kullum na cikin fargaba sakamakon karairayin da’akeyi cewa za’akai musu hari, ya yi kira ga jama’ar yankin da su yi watsi da irin wadannan karairayen da cewa basu da tushe.

“a wasu gurare da dama, lamarin akwai fargaba sosai akan asalin yadda hare-haren suke, saboda mutane suna karamin gari, basu da kwanciyar hankali don haka suke komawa su hadu da wasu suyi yawa, amma muna kame makasan kusan kullum, ina shaida maka yanayin bai munana kamar yadda ake cewa ba, saboda jami’an tsaro suna biye da lamarin.

Tuni dai direbobi sun takatar da bin babban hanyar Numan-Mayo-Lope, sakamakon datse hanyar da mahara keyi suna kashe matafiyar da basusan hawa basusan sauka ba a yankin.

Ko a kwanan baya ma, wasu ‘yan bindigar da’ake zargin matasan Bachama ne, sun kashe wani jami’in soja da direbansa a garin Opalo cikin yankin karamar hukumar Numan, inda aka jefar da gawarsu cikin kogi.

Faruwar lamarin dai yasa jami’an sojojin da suka fusata, kone gidaje da dama a garin, bisa kashe musu abokin aiki, batun da shugaban rundunar soja ta 23 dake Yola Muhammad Bello, ya karyata.

An jima dai ana samun tashe-tashen hankula tsakanin manoma da Fulani makiyaya a yankin, sakamakon rikici kan burtalin shanu, lamarin da ya sabba asarar rayukan daruruwan jama’a da dukiyoyi da dama.

Ko a ‘yan kwanakin nan wasu da’akejin Fulani makiyaya ne sun kai hari kan kauyukan Kolo da Douwaya cikin karamar hukumar Guyuk, inda suka kashe mutum biyar.

Kokarin jin tabakin shugabannin kananan Demsa, Lamurde da Numan kan batun ya cutura domin kuwa sunki amsa kiran waya.


Advertisement
Click to comment

labarai