Connect with us

LABARAI

Kungiyar Kwadago Ta Kulle Ofisoshin MTN A Bauchi

Published

on


A Jiya Litinin ne kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka garkame dukkanin ofisoshi da shagonan kamfanin sadarwa ta MTN a jihar Bauchi bisa gaza bai wa ma’aikatan MTN zarafin shiga kungoyin da suke so wanda hukumar gudanarwa na kamfanin suka yi.

Kungiyoyin kwadagon sun bayyana cewar daukan matakin ya zama tilas idan aka yi la’akari da muhimmancin kungiya ga dukkanin ma’aikacin da ke aiki a karkashin wata ma’aikata, suka nuna kin baiwa ma’aikaci zarafin shiga kungiyar da yake so a matsayin take masa hakki da kuma danne masa ‘yanci da walwalarsa.

An dai wayi gari ne kawai da ganin ofisoshin a kulle, inda kungiyoyin suka hana  kowani ma’aikaci ko ma’aikaciya isa ga ofisoshin nasu domin gudanar da aikinsu kamar yadda suka saba, lamarin da ya tilasta wa ma’aikatan MTN din koma gidajensu a yayin da wasu kuma suka yi ta bulayi a kan titina ba tare da gudanar da aikin da suka saba yi ba.

A bisa haka ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban hadakan kungiyoyin kwadago na jihar Bauchi wato NLC, Kwamared Hashimu Muhammad Gital don jin dalilansu na daukan wannan matakin, inda ya bayyana hakan a matsayin cika umurni da suka samu daga uwar kungiyoyinsu ta kasa.

Ya ce, “Dalilinmu na rufe ofisoshin wannan kamfanin na MTN shine hukumar gudanarwa na wannan kamfanin bata yarje wa ma’aikatan da suke aiki a karkashinta suna hada kungiyarsu ko su shiga kungiyoyin da suke so ba; rashin hada kungiyarsu ba zai basu damar yin gwagwarmayar neman hakkinsu akan aiyukansu ba.

“Saboda haka, dokar kasa ta baiwa dukkanin ma’aikacin da yake da sha’awar shiga kungiya ya shiga kowace kungiyar da ke so domin bidar hakkinsa idan hakan ya taso; ita kuma wannan kamfanin tun zuwanta Nijeriya an buga-an-buga da ita sun ki bayar da izini wa ma’aikatansu da su kasance a kungiyance wacce za take kula da hakkin ma’aikatan. A don haka ne aka bamu umurni mu rufe kamfanin gaba daya,” In ji Gital.

Shugaban hadakan kungiyoyin kwadagon  ya ci gaba da bayanin yadda NLC da TUC suka tashi tsaye a wannan lokacin domin tabbatar da kowace ma’aikata ko kamfani ta bi wannan tsarin, inda yake bayani da cewa kowace ma’aikata ko kamfanin da bata baiwa ma’aikatanta zarafin shiga kungiya ba da cewar fushinsu na nan take kansu.

Inda ya ce, “Ai dokan Nijeriya ce, matukar kana da ma’aikata a karkashinka da suka kai 50 doka ne a yi kungiya. Don haka sauran kamfanonin da suke da matsala irin na MTN suma za mu iso kansu; saboda kafa kungiya ya kare wa ma’aikaci yancinsa ne, idan babu kungiya a kamfani babu tsarin aiki, a rana daya za a iya cewa an dauki ma’aikaci, a rana daya za a iya cewa an kori ma’aikaci, wanda hakan na cutar da su ma’aikatan da suke zage damtsen suna aiki wa kamfanin, don haka kafa kungiya na da amfani wa ma’aikaci, baya ga ma’aikacin ma kungiya tana amfani wa kasan baki daya,” A cewar shi.

Ya bayyana cewar babu wani tirjiya ko kalubale da suka fuskanta a lokacin da suke kulle ofishoshin kamfanin a jihar Bauchi, ya shaida cewar kowani ma’aikaci ya zo aiki ya yi tozali da su kai tsaye yakan kada wa rigarsa iska ne ya juya.

NLC ta bayyana cewar mataki na gaba na biye idan kwamfanin bata dau mataki a cikin kasa da kwanaki uku ba, “Kwana uku za a yi ofishoshin nan suna kulle, idan aka yi kwanaki ukun nan za sake zama idan babu wani natija sai a dau mataki na gaba domin mu umurni ne muka samu daga uwar kungiyarmu na kasa,” In ji shugaban NLC na jihar Bauchi.

Duk kokarin da ‘yan jarida suka yi don jin ta bakin babban jami’in da ke kula da kamfanin MTN a jihar Bauchi lamarin ya ci tura, inda ya shaida mana ta wayar tarho cewar na hanyarsa ta zuwa Kano, dukkanin ma’aikacin kamfanin da muka yi tozali das hi a jihar cewa mana suke yi babu wanda ked a izinin magana kan hakan sai dai shalkwatan MTN da ke Abuja.

Wakilinmu ya shaida mana cewar NLC din dai ta manmanna a jikin ofishoshin tana bayyana dalilanta na rufe ofishoshin, inda ta dambara wa ofishoshin MTN din dirka-dirkan makullen.

Kawo lokacin da muke aiki da labarin nan dai ofishoshin MTN suna kulle a tare da aiki komai kashinsa ba, tuni kuma jama’an jihar suka fara nuna tsoronsu kan idan matsalar network ya riskesu babu yadda za su yi domin a gyara musu, kai tsaye wannan rufe ofishoshin zai taba walwalwar abokan huldar kamfanin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai