Connect with us

KIWON LAFIYA

Girman Jiki Na Taimakawa Wurin Hana Haihuwa

Published

on


Wani kwararen likita mazaunin Abuja Dakata Okezie Emenike,  ya sanar da cewar, girman jiki ko rashin jiki yana iya janyo rashin haihuwa.

Emenike ya sanar da hakan ne a ranar asabar data gabata a hirar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa a Abuja, inda yace, mahimmancin shine a sani cewar dukkan girman jiki da rashin jiki ga mata da kuma maza, suna iya janyo masu kasa haihuwa, inda ya kara da cewar yawan kiba da ake gani a zahiri ga maza tana iya janyo masu kasa yiwa mace juna biyu.

Yaci gaba da cewa, a mafi yawancin lokaci kiba ga mata tana iya janyo masu matsalar kasa dauka juna biyu sakamakon wasu sanadaran dake cikin jikin su, har ila yau, girman jiki ga maza zai iya janyo masu matsalar yadda maniyin su zai dinga fita kuma hakan zai iya kashe masu yin wani katabus a lokacin yin jima’i.

A bayani baki  daya, rashin girman jiki za a iya bayar da kwarin gwaiwa akansa don ayi girman jiki, Inda hakan zai iya kara yawan  rashin haihuwa.

A karshe ya bayar da shawara ga masu larurar dasu samarwa da jikinsu kibar data dace dasu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai