Connect with us

LABARAI

Duk Shekara Mutum 72,000 Kansa Ke Kashewa A Nijeriya

Published

on


Tsohon mataimakin shugaban Jami’ar Lokoja, ta Jihar Kogi, Farfesa Abdulmumini Rafindadi, ya bayyana cewa, daga cikin rahotannin cutar kansa 102,000, da akan samu a duk shekara a kasarnan, masu fama da cutar 72,000, ne cikinsu ke mutuwa sabili da rashin kulawa yadda ya dace

Rafindadi, wanda a yanzun Farfesa ne a tsangayar ‘Pathology’ ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya yi wajen taro na 19 na kungiyar likitoci ta kasa, (IMAM), wanda aka yi a Jami’ar kimiyya da fasaha ta Birnin Kebbi, a Jihar ta Kebbi.

Malamin Jami’ar, ya yi bahasi kan asalin abin da ke kawo cutar ta kansa, inda ya alakanta abin da shan taba sigari, da shan giya ga mazaje, Farfesan ya ce, ana samun rahotannin cutar ta kansa da yawa daga mazajen a asibitoci da suka kai kashi 75 zuwa 80.

“Cutar kansa takan haifar da tsoron da ke kaiwa ga mutuwa, rashin kwanciyar hankali, da rashin nu na kauna ga kowa. Yanayin dabi’unmu, muhallinmu, abinci, halayenmu da kuma abubuwan da suka shafi tattalin arziki, duk suna janyo cutar kansa. A yanzun haka, muna samun rahotannin cutar kansa har guda dubu 102,000, a duk shekara, sa’ilin da dubu 72,000, cikinsu duk mutuwa suke yi a duk shekara. Kasha 50 daga cikin wadannan alkalumna ne masu cutar Kansan Nonuwa.”

A na shi jawabin, shugaban kungiyar ta IMAM, na farko, Dakta Salish Ismail, ya bayyana cewa, kungiyar ta gabatar da ayyukan jinkai na kulawa da bayar da magunguna kyauta ga marasa karfi da suka hada har da ‘yan gudun hijira, hatta da ayyukan tiyata ga marasa lafiya masu cutar yoyon fitsari BBF, da sauran cutuka makamantan hakan duk a kyauta.


Advertisement
Click to comment

labarai