Connect with us

LABARAI

Buri Na Taimaka Wa Nakasassu Iri Na –Yahaya Makaho

Published

on


Fatana ko bayan raina ya kasance ba da wake-wake na kadai ake tuna ni ba, ya kasance ana tuna ni ne da wasu ayyukan alherai da na yi a baya. Wannan shi ne kalamin shahararren mawakin nan na hausa, Malam Yahaya Makaho, a sa’ilin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da sabon faifan wakensa da aka yi ranar asabar a babban dakin taro na Umaru Musa ‘Yar’aduwa da ke dandalin Murtala a Kaduna.

Malam Yahaya Makaho, ya ci gaba da bayyana cewa, cikin abin da ya sanya a kullum ake kiranmu nakasassu shi ne, ba wani lokaci da muke yin wani abu na kanmu sai dai a yi mana. Hakan ne ya sanya ni nake son na yi amfani da basirar da Allah Ya bani na wannan dama da nake da ita, wajen ganin ni ma ina taimaka wa mutane kamar yadda wasu ke taimakawa, kuma saboda Allah, ba kawai domin a yayata ba. Domin ko bayan raina ya kasance ana alfahari da ni ba domin wake-wake na ba, ana alfahari da ni ne ta wajan taimaka wa mutane musamman masu nakasa irin nawa.

Ina kuma amfani da wannan daman wajen yin kira ga dukkanin masu nakasa iri na, da mu kasance masu hakuri mu kuma zamanto jajirtattu a kan dukkanin abin da muka san zai taimaki rayuwarmu. Mu kawar da tunanin cewa wai wani zai yi mana, mu yi iya bakin abin da muke iyawa, sai kuma mu barwa Allah sauran.

Ina sane da cewa, akwai mutanan mu da suka iya saka, walda, man shafawa, sabulu da dai sauran sana’o’i kala-kala. Amma abin takaicin shi ne, sam mun kasa samun taimakon da ya kamata daga gwamnatocin Jihohi tare da cewa, sune suka gina makarantun koyar da sana’o’in makarantun da aka koyar da wadannan mutanan. Wanda, da an kirkiri yanda za a amfana da basirar da wadannan mutanan Allah Ya yi masu, da kuma abin da aka koya masu, tabbas da dukkanin kasar ma ta amfana. Domin in har an koyar da kai, sannan sai aka sake ka a igiyar ruwa, musamman ma ga mutumin da yake shi baya gani, to ai ilimin da aka koyar da kai din ba shi da amfani kenan, domin ba zai taimake ka wajen iya rike rayuwarka da ta iyalanka da ma ta sauran ‘yan’uwanka ba, kila har da dan abin da za ka iya taimakawa al’umma.

Hakan kuma ba zai taimaka maka wajen kare mutuncin ka da na Addinin ka ba, ba kuma zai sanya ka iya kare matsalar mutanan da Allah bai yi masu fasahar da Ya ba ka ba, hakan kuma ma bai taimaka wa ita kanta gwamnati ba, domin ba za su daina bara ba.

Dangane da tarin al’umman da suka halarci taron, Malam Yahaya Makaho cewa ya yi, a gaskiya a baya ana ce mani, farin ciki na sawa a yi kuka, amma na kan yi shakkan hakan, amma tabbas a yau na sallama na kuma yarda da cewa lallai farin ciki zai iya sawa a yi kuka. Domin duk da ba gani nake yi ba da idanuna, amma zuciyata tana shaida mani a bisa irin sunayen mutanan da naji ana ambata a wajen taron ya tabbatar mani da irin tarin al’umman da a baya in an ce zan iya tara su, hankali na ba zai iya dauka ba, kuma mutane masu mutunci irin wadannan. Don haka ya yi matukar nuna jin dadi da farin cikinsa gami da godiya ga dukkanin mahalarta taron.

Taron kaddamarwar, wanda aka shirya shi da nufin kafa gidauniyar mawakin wacce za ta rika tallafa wa sauran nakasassu irin sa, ya sami halartar manyan mutane da al’ummu maza da mata masu yawa. Ta sami halartar manyan mutane daga ciki har ma da wajen kasarnan, kadan daga cikin su, sun hada da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, tsohon shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar ta Kaduna, Alhaji Yaro Makama Rigachikun, Dakta Hakeem Baba Ahmad, babban aminin mawakin, Alhaji Nasiru, wanda shi ne babban wanda ya sayi faifan waken a kan tsabar kudi Naira milyan biyu. Hakanan manyan jaruman fima-fiman Kannywood, da suka hada da Hadiza Gabon, Aminu Alan waka da makamantansu tuli duk sun halarci taron.


Advertisement
Click to comment

labarai