Connect with us

LABARAI

Nijeriya Na Asarar Naira Biliyan 300 Duk Shekara Kan Zazzabin Maleriya –Obasanjo

Published

on


Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya ce, Nijeriya na yin asarar fiye da Naria Biliyan 300 a duk shekara wajen rigakafi da maganin cutar maleriya da sauran cututtaka masu saurin yaduwa.
Cif Obasanjo ya yi wannan bayanin ne a yayin kaddamar da gidauniyar gida jami’a na musamman na kiyon lafiya “Unibersity of Medicine and Medical Studies” na hukumomin asibitn tarayya na Abeokuta suka shirya ginawa,(Federal Medical Centre, Abeokuta.)
Bikin a gudana ne inda aka shirya gina jami’ar dake kauyen Ajibayo, a kan hanyar OGTB-Ajebo, Abeokuta.
Tsohon shugaban kasar ya ce, Nijeriya na fuskantar matsaloli a fannin samar da kiwon lafiya da suka hada da mace-macen mata masu haihuwa da mace-macen jarirai da cutukar da basa yaduwa tsakanin al’umma da sauran cututtukan dake yin barazana ga rayuwar jama’a.
Ya kuma kara da cewa, kashi 43 na daukacin ‘yan Nijeriya basu da daman samun rowan sha mai tsafta da sauran harkokin samar da kiwon lafiya.
Ya kuma ce, a kan haka kasar nan na yin asarar fiye da Naira Biliyan 300 wajen yin maganin cututukan da za a iya yin maganinsu in har da an samar da cikakken kudaden ga bangaren samar da kiwon lafiya a kasar nan.
Ya ce, “Nijeriya na asarar fiye da Naira Biliyan 300 a duk shekara a wajen karewa da yin maganin cutar maleriya, tare da asarar da ake yin a rashin zuwa aiki ga wadanda suka kamu da cutar. Wadannan lamarin yana kara muni ne in aka lura da tsananin lallacewar da ake dasu a fannin samar da koeon lafiya na kasar nan.
“A bayyana lamarin yake cewa, kashi 43 na ‘yan Nijeriya basu samun tsaftatatacen ruwan sha, kashi 37 kuma basu cikakken harkokin tsaftace inda suke, kashi 40 kuma gaba daya basu iya samun magani daga cibiyoyin samar da kiwon lafiya na kasa.
“Baya ga wadannan cututtuka an kuma samu karuwar bazuwar cututtukan da basu yaduwa tsakanin al’umma irinsu ciwon suga da ciwon hawan jini da ciwon koda da kuma cutar kansa na nono ga mata da kansar mahaifa da kuma cutar mafitsara da kansar mafitsara ga mazajenmu, wadanna gaba daya abin tayar da hankali ne.”
Gwamnan jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amosun, ya ce gwamnatin jihar zata bayar da gudummaar Naira miliyan 50 don gina jami’ar “Unibersity of Medicine and Medical Studies” ya kuma yi alkawarin bayar da gudummawar Naira Miliyan 10 a kashin kansa.


Advertisement
Click to comment

labarai