Connect with us

LABARAI

2019: PDP Da Jam’iyyu 41 Za Su Tsayar Da Dan Takara Daya Bello Hamza,

Published

on


A shirye shiyen zaben shugaban kasa na shekarar 2019, babbar jam’iyyar adawa PDP ta shirya hada hannu da jam’iyyu 41 don fito da karfarfar dan takarar shugaban kasa da zai iya fuskantar jam’iyya mai mulki.
Burin wannan shirin shi ne hada hannu a fito da dan takara daya da zai yi takara a karkashin daya daga cikin jam’iyyun hadakar.
A kan haka da kuma burin ganin sun fatattaki shugaba Muhammadu Buhari, jam’iyyun suna ta shiye shiye da tarurruka don ganin hakan nasu ya cimma ruwa.
Taro na baya bayan nan da aka gudanar a gidan tsohon ministan kasashen waje Cif Tom Ikimi ranar Laraba ya samu halartar wakilai daga jam’iyyun dake cikin hadakar da dama.
Majiyarmu ya bayyana mana cewa, jam’iyyar PDP ta samu wakilcin shugaban kwamitinta a kan ganin nasarar hadakar kuma tsohon gwamnan jihar kuros Ribas, Sanata Liyel Imoke.
Haka kuma taron ya samu hakartar sakataren kasa na jam’iyyar Sanata Ibrahim Tsauri da mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a Barista Emmanuel Enoindem da tsohuwar shugaban mata na jam’iyyar Ambasada Kema Chikwe da kuma Ambasada Aminu Wali da sauran manyan ‘yan jam’iyyar ta PDP.
Majiyar ta kuma ce, jam’iyyar APP ta samu wakilcin shugabanta ne Cif Ugochinyere Ikenga.
Daga nan majiyar tamu ta kuma kara da cewa, an shirya wani taron jiya da misalign karfe 5 na yamma, amma har zuwa hada wannan rahoton babu tabbacin ko an gudanar da taron ko a a. shugaban daya daga cikin jam’iyyum wanda kuma ya bukaci mu sakaya sunansa ya ce, “Shirin da muke yi ba dunkulewa muke kokarin yi ba amma muna shirin yin hadaka ne na fiye da jam’iyyu 42 dake da cikakken ragista da zasu kalubalanci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, jam’iyyun sun shiya a bisa radin kansu na ceto Nijeriya daga halin da take ciki a halin yanzu.
“Mun shirya samar da gwamnatin hadin kai ne “Gobernment of National Unity”. Buhari na kan hanyarsa na fita ne daga gidan gwamnati, zai sha kaye kamar karamin yaro a fagen dambe, shirinmu shi ne na n takara daya tare da goyon bayan dukkan jam’iyyun siyasar dake cikin hadakar don fuskantar Muhammady Buhari, dan takarar na iya zama wani ne daga jam’iyyar PDP ko SDP ko LP ko kuma PPA.”
Bayan jam’iyyar PDP, sauran jam’iyyun dake cikin wannan hadakar sun hada da jam’iyyar Accord Party,AP da Action Alliance, AA da Adbanced Congress of Democrats da ACD da Alliance for New Nigeria, ANN da kuma Adbanced Peoples Democratic Alliance, APDA da All Progressibes Grand Alliance, APGA da African Peoples Party, APP da Democratic Alternatibe, DA da Democratic Peoples Congress, DPC da Democratic Peoples Party, DPP.
Sauran sun hada da Fresh Democratic Party, FDP da Hope Democratic Party, HDP da Labour Party, LP da Social Democratic Party, SDP da Kowa Party, KP da Modern Democratic Party, MDP da Mega Progressibe Peoples Party, MPPP da Peoples Democratic Mobement, PDM, da Socialist Party of Nigeria, SPN da sauransu.
Wata majiya daga cikin jam’iyyar SDP ta bayyana mana cewa, “Jam’iyyun siyasa sun yanke shawarar bin tsarin daya kai ga kayar da jam’iyyar PDP ne shekara 3 da suka wuce. Zasu samu cikkaken karfi in suka shiga zabe a hade amma za su fuskanci rauni in suka shiga zabe a daidaikunsu. A saboda haka ne suke taro akai akai, ina kuma shaidawa ‘yan Nijeriya cewa, lallai suna sanya kasa ne a kan gaba dukkan shawarwarin da suke yi.”


Advertisement
Click to comment

labarai