Connect with us

LABARAI

Sarkin Zazzau Ya Kuduri Aniyar Tallafa Wa Mahaddata Alkur’ani

Published

on


Mai mattaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, ya kuduri aniyar ci gaba da tallafa wa Kungiyar Mahaddata Alkur’ani reshen jihar Kaduna, domin su sami saukin gudanar da ayyukan ciyar da addinin musulunci da kuma musulmi gaba a fadin jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya. Mai martaba Sarkin Zazzau ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar reshen jihar Kaduna a fadarsa da ke birnin Zariya.
Alhaji Shehu Idris ya ci gaba da cewar, babu shakka ya san ayyukan ciyar da musulunci gaba da wannan kungiya ta ma mahaddata ke yi shekaru da dama da suka gabata, a jihar Kaduna, musamman na koyar da al’umma da kuma yin wa’azin da ke ciyar da addinin musulunci gaba ta ko wane fanni na rayuwar al’umma, musamman ma Musulmi.
Kan haka ne mai martaba Sarkin Zazzau ya kara da cewar, fadarsa na bude ako wane lokaci, domin wannan kungiya ta sadu da shi, a kan duk wasu abubuwa da za su ciyar da musulunci da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar Kaduna da kuma Nijeriya kafatan.
A dai jawabin mai martaba Sarkin Zazzau, ya yi kira ga shugabannin wannan kungiya da su ci gaba da yin addu’o’in tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a daukacin Nijeriya, ba masarautar Zazzau ko kuma arewacin Nijeriya kawai ba.
Game da matsalolin da makarantun da Mahaddatan ke koyarwa kuma, mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris,ya umurci shugabannin kungiyar das u kai ma sa daukacin sunayen makarantun da suke koyarwa, ya ce, da zarar sunayen sun je wajensa zai ba su tallafi na musamman, domin su sami damar koyar da daliban a cikin sauki a nan gaba.
A karshen jawabin mai martaba Sarkin Zazzau, ya yi kira ga daukacin mambobin da suke wannan kungiya ta mahaddata, da su rika yi wa kasa da shugabanni addu’o’in da za su zama silar murkushe ko wace irin matsala da ta so wa kasa, da kuma al’ummar kasar.
Tun farko a jawabinsa shugaban kungiyar na jihar Kaduna, Gwani Nabara Naziru Birnin Gwari ya bayyana cewar, sun kai wa mai martaba Sarkin Zazzau wannan ziyara ce domin nuna gamsuwarsu da shugabancin adalci da hakuri da kuma hangen-nesan da Sarkin ke da shi, shekara 43 ya na sarauta a masarautar Zazzau.
Gwani Nabara ya tabbatar da cewar, salon mulkin da mai martaba Sarkin Zazzau ke yi,al’ummar Nijeriya ne ke amfana da shi, ba al’ummar masarautar Zazzau kawai ba.
Cikin wadanda ke cikin tawagar shugaban Kungiyar, a kwai sakataren kungiyar Alaramma Bashir Halidu Cukun da Alhaji Lukman da kuma daukacin shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar Kaduna 23.


Advertisement
Click to comment

labarai