Connect with us

LABARAI

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama ‘Yan Damfara A Sakkwato

Published

on


Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta bayyana cewar ta kama mutane da dama wadanda suka yi kaurin suna wajen aikata ayyukan assha a Jihar.
Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar, Mataimakiyar Sufuritandan ‘Yan Sanda DSP Cordelia Nwawe ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a ta na cewar daga cikin wadanda ake zargin akwai Usman Danmaliki wanda ya yi fice wajen damfarar al’ummar Rikina da kewaye da ke Karamar Hukumar Dange-Shuni a Jihar Sakkwato wanda ke kama mutanen kauyen ta hanyar labewa da cewar shi jami’in shari’a ne yana karbar kudaden hannun su.
Ta kuma bayyana cewar sun kuma kama wani mai suna Mamuda Hamza da katin shaida na Rundunar wanda yake amfani da shi wajen sojan gona yana damfarar mutane kudade da sunan cewa shi jami’in Dan Sanda ne.
“Mamuda Hamza yana yaudarar mutane wadanda ba ‘yan Nijeriya ba musamman ‘yan kasashen Chadi, Mali da Jamhuriyar Nijar. An kama shi ne a yayin da muka yi masa kwanton bauna bayan ya damfari wani dan Chadi kudi har naira miliyan 1.2.” In ji Cordelia.
Jami’ar ta Hulda da Jama’a ta kuma bayyana cewar Rundunar ta kuma kama wasu tsagerun matasa biyar wadanda aka fi sani da ‘Area Boys’ tare kuma da kama wasu matasa biyu Abdullahi Abubakar da Nura Lawal wadanda aka kama da kulli 350 na abinda suke zargin tabar wiwi ce wadanda ta ce duka za a gurfanar da su a gaban Hukuma.
Ta ce Kwamishinan ‘Yan Sanda Mista Murtala Usman Mani ya sha alwashin ci-gaba da sanya idanu tare da gudanar da bincike domin kare lafiyar al’umma da dukiyoyinsu. A kan wannan ta bukaci al’ummar Jihar da su ci-gaba da baiwa ‘Yan Sanda bayanai masu muhimmamci wadanda ke iya taimakawa wajen kama wadanda ke aikata ayyukan assha a fadin Jihar.


Advertisement
Click to comment

labarai