Connect with us

LABARAI

Kungiyar Red Card Ta Yi Taron Wayar Da Masu Zabe A Bauchi

Published

on


Kungiyar Red Card Mobement mai rajin wayar da kan jama’a domin zabar shugabannnin da suka taka rawar gani tare da kin sake zaben duk wani wakili ko shugaban da bai taka rawar gani ba, ta gudanar da taron wayar da kan jama’a game da yadda za su zabi shugabannin da ke sauke nauyin da aka dora musu don a samu ingancin wakilci da dorewar mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.
Gangamin wanda aka gudanar da shi ranar asabat a mashigar dakin taro na Multi Purpose da ke kusa da kasuwar Wunti a cikin garin Bauchi ya ja hankalin jama’a da su himmatu wajen yin rijistar jefa guri’a wato katin zabe don kowane dan kasa ya samu damar zabar wakilin da zai taimaka wajen ci gaban yankinsa da kasa baki daya.
Don haka shugabar gangamin kuma wakiliyar kungiyar ta Red Card Sarauniya Comfort Atah cikin jawabinta ta bayyana cewa sun shirya wannan gangami ne a jihohi 36 na Nijeriya don wayar da kan mutane tare da basu dama su yi bayani game da matsalolin da suke fiskanta da wakilan su. Don haka ta ja hankalin mutane da su kasance masu hakurin zama da juna tare da yin zabe bisa ra’ayi don kawo shugabannin da za su taimaki mutane ba wadanda idan sun tafi ba za su sake waiwaitar mutanen da suka zabe su ba.
Don haka ta kara da cewa rike katin zabe da muhimmanci shi ne babban makami da zai taimakawa mutane su nuna darasi mai karfi ga duk wani dan siyasar da aka zaba ya gaza cikawa ko sauke nauyin da aka dora masa. Ta shawarci mutane da su yi siyasa ta akida wacce za ta timake su samun shugabanni na gari da za su sauke amanar da aka dora musu don ciyar da mutane gaba. Don haka ta bayyana cewa wannan gangami tare da raba jan kati wa mutane sun bayar ne don a rike saboda a kowane lokaci ya rika tunasar da mutane idan sun zo jefa guri’a don su yi waje da duk wani wakili da suka zaba amma ya gaza sauke nauyin da aka dora masa.
Don haka wannan kungiya ta jan kati ta fito don wayar da kan jama’a masu guri’a kamar yadda ake tunasar da dan wasan kwallo da ya gaza bin doka yadda daga bisani ake ba shi jan kati haka suke son mutane su ba duk wani dan siyasa jan kati matukar bai taka rawar da ta dace ba don sauke nauyin da aka dora masa.
Hajiya karima Ibrahim cikin jawabinta ta bayyana fito da wannan manufa ta jan kati wata sabuwar hanya ce don zabar mutanen kwarai a siyasance don kawar da mutane marasa kishi da cika alkawari, saboda haka ta ja hankalin masu zabe su sani guri’ar su ‘yanci ne a gare su na zabar shugaban da zai taimake su wajen samun wakilcin da zai ciyar da jama’a da kasa gaba
Mista Kingsley Yalem shima cikin jawabin sa ya bayyana cewa lokaci ya yi da mutane za su gane suna yin zabe ne don su amfana daga wakilcin ‘yan siyasa ba domin shugaban da aka zaba ya tafi ya azurta kansa ba tare da kawo ci gaba wa mutanen sa ba. Don haka ya ce daukar matakin gaggawa na wayar da kan mutane yadda za su cire duk wani shugaba da bai kyauta musu ba ya zamo wajibi don haka ya gargadi mutane su kasance masu hakuri har zuwa lokacin da za su dauki fansa kan duk wani shugaban da bai sauke nauyin shugabancin da ya yi alkawari wa mutanen sa ba ta hanyar taruwa a bashi jan kati a ranar zabe.
Shi ma Malam Bako APC wani mutum da ya halarci wajen wannan gangami ya kuma bayar da tasa gudummowa lokacin da aka ba shi dama ya bayyana cewa a kullum yana jiran lokacin da zai samu irin wannan dama don haka ya tofa albarkacin bakin sa tare da jan hankalin jama’a da ke wajen gangamin kan su dauki shawarwarin da ake basu, don kowane mai zabe ya yi zabe ne da nufin rayuwarsa ta inganta amma lamarin ya zamo tamkar bauta don haka ba za su sake wannan kuskure ba ya kamata a duk lokacin da dan siyasa ya zo da nufin a zabe shi kowa ya duba irin gudummowar da ya bayar don ci gaban mutanen sa kafin a kai ga zabarsa don ya wakilci mutane, hakan shi zai hana sakaci da cin amanar da ‘yan siyasa ke yi wa masu zabe.


Advertisement
Click to comment

labarai