Connect with us

KIWON LAFIYA

Hanyoyi Mafi Sauki Na Dakile Kamuwa Da Cututtukan Sanyi

Published

on


Ina ganin wannan ne daidai lokacin da ya dace inyi shirhi akan wannan maganar.
Shin ko ka lura cewar duk inda kaje zaka ga mutane suna yin tari da mura da da yin nufashi kadan-kadan da yin kakari saboda kaikayin da suke ji a makogwaron su dake haifar da zazzabi da sauran su.
A yayin wata ziyara danaje a wani shagon sayar da magani naga yadda mutane suke ta tururuwa zuwa sayen magunguna, wanda inda sunyi amfani dana gargajiya za su fi samun saukin murar cikin sauri da kuma sauki.
Mafi yawancin shagunan magun gunan, har ta kai ta komo sun fara karancin magun gunna na mura.
A irin wannan yanayin kamata ya yi mu rungumi yin maganin mura ta hanyar gargajiya.
Maganar gaskiya itace, idan kana cin abinci ka koshi kuma kana da koshin lafiya,dan digo kadan zai taimakawa garkuwar jikin ka wajen kamuwa da alamomin mura.
Amma idan kana zuwa gun likita ya dubaka akwai alamar cewar jikin ka yana neman taimako kuma garkuwar jikin ka za ta daidaitu.
Amma ana son ka gane cewar, wannan ba ya dakatar da kai daga zuwa ganin lokita bane.
Kada wannan ya kasance tunanin ka na farko, amma idan ka sani wannan zai kara taimaka maka. Zai iya kasancewa sanyi ne, amma ba numfashi ba.
Alamar ta mura zaka dinga jin zazzabi da kasala. Sai dai, abinda zaifi sauri daga bangaren hade da sauran wasu hanyoyi kanana masu sauki na warkar da murar zai iya janyo maka wata matsala.
Shin sanyi da ka saba ji ne ko kwayar cutar mura ce?
In har alamomin sun wuce wuyanka da jin zafi a makogwaro da wahalar numfashi da tari, tabbas alamace ka kamu da mura.
Idan kuma duk kana jin wadannan alamomin, har da jin zazzabi da ya kai nauyin ma’aunin yanayi (38.80) nauyin ma’aunin yanayi (102ûF) ko kuma yawan jin ciwon kai da ciwon gabban jiki da yawan jin kasala da gudawa da amai, zaka iya kasancewa kana da kwayar ta mura.
Sanyin da akafi sani kwayoyin 200 da ban-da-ban na mura zai kuma iya shafar bayan gidanka kuma kwayoyin cutar zaka iya yadasu zuwa ga mutane.
Mutane masu karancin garkuwar jiki, sun fi saurin kamuwa da da sanyi.
Bugu da kari, abubuwan dake nuna an kamu da sanyi sune, rashin jin barci da jin gajiya da yin bahaya.
Labari mai kyau shine, akwai hanyoyi da dama na gargajiya na magance jin sanyi a kai da za su taimaka maka wajen magance alamomin.
Abincin da Kake ci:
1. Sanadarin (Bone Broth) yana kunshe da sanadari na (amino acids) da kuma sanadarin (minerals) da za su taimaka maka wajen samun karfin garkuwar jiki, kuma ya kamata ka dinga shan miyar da dake dauke da sanadarin ainahin sanadarin( bone broth) da kuma kayan lambu.
2. Isashen ruwa: isasseh ruwa a jikin ka zai taimaka wajen fitar da dukkan wani kwayar cuta daga cikin jikin ka.
Ka yi kokari wajen shan ruwa a kalla kofi takwas duk bayan awa biyu.
3. Shan ruwa mai zafi tare da lemo da zuma –Wadannan za su taimaka maka wajen rage majina sannan kuma ka kasance kana da sauran ruwa a jikin ka.
4. Jinja– ka hada shayi da jinja da zuma wadda bata da gauraye.
5. Tafarnuwa da Albasa – dukkan wadannan kayan lambun suna taimakwa garkuwar jikin mutum kuma suna taikamawa daga wajen bada kariya daga kamuwa da kwayoyin cuta musamman ganin suna dauke da sanadarin (allicin).
Abincin da ya kamata mutum ya kiye ci:
•Sikari – yana rage sanadaran sel na cikin jinin mutum wanda ke taimakwa wajen yakar wasu cututtuka a cikin jikin mutum.
• Kayan Lambu da aka sarrafa su zuwa kayan zaki –koda yake, kayan zaki na lemo yana dauke da wasu sanadarai na Bitamin C, kuma baida karfi a cikin Bitamin C gaba daya ko kayan lambu.
Idan kana son ka sha kayan marmari da aka maida dasu kayan zaki na ruwa, ka dinga sirka shi da ruwa.
•Kayan da masana’antar sarrafa kayan lambu zuwa kayan zaki da sauran su, suna haifar da majina.
• Abincin da ake sayarwa a shaguna– basu dauke da sanadarin (calories) da zai taimakawa garkuwar jikin ka.
• Hatsin da aka sarrafa shi– kamar Burodi da da hatsi da alkama da fulawa suna saurin komawa Sikari da gajiyar da garkuwar jikin.
Sanyi da alamomin sa da aka fi sani:
Wata kila ka taba fuskantar wadannan alamomin :
Numfashi
Cusehawar hanci
Hancin ka ya yi ta yoyo
Jin zafi a makogwaron ka
Tari
Jin ciwon kai
Jin ciwo a jijiya
Zubar majina
Ragewar jin cin abinci
Fitowar kuraje a makogwaro
Idonka ya dinga yin ruwa
Abinda zaka iya yi akan sanyi da kwayar cutar sanyi:
Don magance jin ciwon makogwaro kana iya yin amfani da ruwan dumi mai nauyin mili lita 250 ta hanyar shan ruwan da chokalin shan shayi hade da gishiri sai dai gishirn baya warkar da jin zafin.
Ka kara da lemon zaki da ka matse a cikin kofi hade da ruwan dumi zai taimakawa jin zafin da kake ji a makogwaron ka.
Wannan yana taikamawa wajen yakar dukkan wasu kwayoyin cuta. Miyar farfesun kaji itama tana taimakawa musamman wajen fitar majina daga hanci haka miya mai zafi tana taimakawa wajen fitar majina.
Miyar mai zafi tana dagargaza majinar dake cikin hancin tare da sanya tafarnuwa a cikin miyar za ta karawa jiki karfi.
Tafarnuwa tana kashe kwayoyin cuta da taimakawa wajen fitar da sanadarai da suka mutu a jikin mutum.
Ka sanyawa miyar taka barkuno za ta taimaka wajen rage maka cinkoso a hancin ka.
Da zarar ka ankare da kwayoyin cuta na sanyi, ka fara shan magani mai nauyin 500 dake dauke da Bitamin C har zuwa tsawon kwana hudu zuwa shida.
Idan ka kamu da zawo sai ka yanke shan maganin. Sanadarin (Goldenseal) yana taimakawa garkuwar jiki da kuma yakar cututtukan sanyi. Da zarar ka fara jin sanyi, sai kasha kwayar magani na nauyin mili giram 125 sau biyar har zuwa tsawon kwana biyar.
A lokacin daka fara ganin kwayar cutar ta mura, kasha maganin daga ashirin zuwa talatin kamar sauku zuwa hudu har tsawon kwana uku. Maganin na (Elderberry) ana amfani dashi sasai wajen yakar kwayoyin cuta na sanyi.
Yin amfani da tafarnuwa shi ma yana taimakwa sosai
Amma akan cushewar da tay kamari, ka sayi sabuwar Jijiyar Jinja ka nikata ka dinga ci kadan-kadan. Don kaucewa rikicewar ciki, ka jira sai ka gama cin abinci tukunna.


Advertisement
Click to comment

labarai