Connect with us

LABARAI

Dalilin Da Ya sa Nijeriya Ke Cikin Tashin-Tashina –Sule Lamido

Published

on


Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma Dan Takarar Shugabancin Kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya ta’allaka yawaitar kashe-kashe da tashin-tashina da ke faruwa a Nijeriya ga kasawar Shugaba Muhammadu Buhari wajen gudanar da mulki nagari yana cewar ko wace kasa ta na tafiya ne a bisa ga yadda shugabanta ke gudanar da ita
Lamido wanda ya ziyarci Sakkwato a rangadin da yake yi na tuntuba game da aniyarsa ta takarar mukami mafi daraja ta daya a kasar nan ya bayyanawa manema labarai cewar kashe-kashen da ke faruwa da bakar kwakwar da al’umma ke sha suna faruwa ne a bisa ga turbar da jagoran kasar ya dora ta.
Ya bayyana cewar yanzu fa lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su fuskanci gaskiyar lamari su kuma tattauna kan muhimman al’amurra domin samun ci-gaba mai amfani da dorewa.
Babban jigon dan siyasar ya bayyana cewar bayan nazarin diddigi, ‘yan Nijeriya za su yadda da shi cewar har yanzu jam’iyyar PDP ce mafitar magance matsalolin Nijeriya da al’ummarta.
“Jam’iyyar PDP ita ce tarihin Nijeriya domin ita kadai ce jam’iyyar da ke kaunar talakawa a cikin zuciya wadda kuma ita ce uwa ga dukkanin jam’iyyun siyasa a kasar nan wadda aka kafa a bisa ga hadin kai da zummar bunkasa ci-gaban al’umma amma jam’iyyar APC, jam’iyya ce ta tsana, kiyayya da kuntatawa.” Ya bayyana.
Ya ce “Kowace kasa ta na koyi da halaye da dabi’un shugaban ta. Idan Shugaban Kasa ya kasance mutum mai halaye nagari, mai son jama’a, mai taimako to haka al’ummarsa za su kasance. Amma idan Shugaba ya kasance mai tsana da nuna kiyayya to haka jama’arsa za su zama kuma su kasance.”
Ya ce yanayin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke gudanar da shugabancin kasar nan ne ya haddasa kisan al’umma da ayyukan ta’addanci a sassan kasa bakidaya.
A kan dalilin da yasa ya fito takara, tsohon Ministan na Al’amurran Kasashen Waje a zamanin Gwamnatin Obasanjo ya bayyana cewar idan aka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa zai kawo karshen mulkin danniya da zalunci tare da magance kashe-kashen al’ummar da a yanzu ya zama abin da ke faruwa a kullum.
“Abin da kawai zai kawo karshen shu’umin bahagon mulkin APC shine dawowa da PDP saman mulki. Mun riga mun ga yadda APC ta fadi kasa warwas wajen sauke nauyin da aka dora mata domin sun dauki tsana da kiyayya sun sa a zukatansu wanda shine ke cutar da ‘yan Nijeriya.”
“Idan aka zabe ni a matsayin Shugaban Kasar Nijeriya abu na farko da zan fara yi shine zan kira taron dukkanin masu ruwa da tsaki daga kowane bangare domin tattauna matsalolin da ke akwai wadanda ke barazana ga hadin kai da zaman lafiyar kasar nan.” In ji Lamido.


Advertisement
Click to comment

labarai