Connect with us

MAKALAR YAU

Daga Ina Yaro Ke Koyo Dabi’un Banza?

Published

on


Babban abun da ya fi damun mutanen arewacin Nijeriya a wannan zamani shi ne yawaitar mutuwar aure. Musamman a babbar cibiyar kasuwancin Arewa, wato kanon dabo, al’amarin ya fi kazanta a can. Ta yadda kungiyar zawarawa mai karfi da ake da ita a kasar hausa, wacce ked a cibiya a Kano ita ce mafi girma da tasiri.
Wannan matsala na mutuwar aure da dandazon zawarawa da kullum ake kara samu ne kuma aka samu wani shiri na aurar da zawarawa, ta hanyar bin salo da dabarun da za a iya samu su shige a cikin sauki ba tare da an wahala ba, sannan kuma aka sa dokoki masu tsauri akan wadanda su ka aure su din.
Yunkurin jajircewa akan neman mafita ga zawarawan Kano kadai ya isa ya nunawa duniya cewa akwai matsalar mace – macen aure a Arewacin Nijeriya.
Watakila ba kowa ke da masaniyar illar rabuwar auren miji da matan da aka samu haihuwar ‘ya ‘ya a tsakaninsu ba. mafi karfin muni shi ne ya kasance auren ya mutu ne alhali ‘ya ‘yan ko kuma dansu yana cikin shekarun yarinta, wanda bai kai shekarun da za a kira shi mutum mai cikakken hankali ba.
Yaro a irin wadannan shekarun, wanda a Nijeriya doka ta tanada cewa duk yaron da shekarunsa su ke kasa da 18 ba za a yanke mai hukunci dai dai da babban mutum ba. idan ya aikata laifi kamar sata, da sauransu ba zai yiwu a kai shi kotu ba ballantana a kai shi gidan yari.
Dalilin da ya sa ba a yankewa yaro dan kasa da shekaru 18 hukunci dai dai da na wanda yah aura wadannan shekaru shi ne bisa la’akari da yanayin kwakwalwar yarinta ta wanda bai wuce wadannan shekaru ba.
Masana a fannin ilmin halayyar jama’a (Sociology) su kan kira yaro dan kasa da wadannan shekaru da suna ‘Jubenile’, a lokacin da ya sabawa dokoki ko kuma ya aikata wani mummunan laifi ba kiranshi da ‘crime’ sai dai ‘Delinkuent’. Ma’anar ‘delinkuent’ shi ne laifin da yaro wanda bai mallaki hankalinshi ba ya aikata.
Shekarun yarinta shi ne mafi muhimmanci shekaru a rayuwar mutum, a wannan shekaru ne yaro ya ke samun tarbiyyar yadda zai assasa tubalin rayuwarshi.
La’akari da haka ne Masana a fannin ilmin kimiyyar halayyar jama’a (Sociology), su ka yi kokarin yin bincike mai zurfi akan dalilan da su ke sa yaro ya zama mara tarbiyya da hanyoyin da ke aukar da hakan domin a kiyaye.
Cikin abubuwan da masana su ka yi nuni wanda kuma yake tsananin tasiri a gurbata dabi’ar yaro shi ne ya taso a yanayin da mahaifinshi da mahaifiyarshi ba su tare. Walau ko daya daga cikin iyayen yaron sun rasu, ko kuma sabani ya sa aure ya mutu.
Kasantuwar rashin daya daga cikin iyaye biyu, mahaifi ko mahaifiya wani abu ne da mutane su ka shaidi cewa yana tasiri sosai wurin gurbacewar tarbiyyar yaro, matukar ba a dauki matakai masu karfi wadanda su ka dace ba.
Ban da wannan kuma akwai batu mafi karfi wanda kuma Masana a fannin ilmin halayyar jama’a din su ka fi mayar da hankali akai, shi ne mu’amalar da ke aukuwa tsakanin yaro da wasu yara, wadanda a wasu lokutan su ke rayuwa da su a matsayin abokai.
Ya fi sauki yaro ya koyo mummunan dabi’a ko kuma tarbiyyarshi ta gurbace sakamakon yin tarayya da sauran yara. [abi’ar abokai sun fi tasiri akan yaro fiye da duk wata dabi’a da zai iya gani a lokacin yarintarshi.
A Nijeriya, sakamakon matsanancin talaucin da ake ciki ya haifar da wasu halaye wadanda ba kowane ya ke son kasancewa a cikinsu ba.
Misali, ba kowa bane ke son zama a gidan haya mai mutane da yawa, domin cakuduwar mutane daban daban a gida daya yana haifar da musayar dabi’a tsakanin wannan iyalin da wancan iyalin.
Irin gidajen hayan da ake da su a Nijeriya, wanda kashi 75 na talakawa ke rayuwa a cikinsu. Gidaje ne da babu yadda za a yi mutum ya iya hana danshi yin mu’amala da sauran ‘ya ‘yan gidan.
Idan kuma gidan mutum shi kadai ne ba gidan haya bane, yanayin unguwannin da ake da su yanzu a Nijeriya, akwai bambanci tsakanin na talakawa da masu kudi. a unguwannin talakawa ko da a ce gidan mutum shi kadai ne a ciki, to muddin danshi yana fita waje, zai hadu da yara wadanda tarbiyyarsu za ta iya yin tasiri akan nashi.
Idan aka kiyaye dukkan wadannan. Ya kasance mutum a unguwannin masu hannu da shuni yake zaune, matsalar gurbatar tarbiyyar danshi na iya aukuwa ne yayin da dan ya je makaranta ya hadu da abokai mabambanta, a cikinsu idan ba sa a ba, za a iya samun matsala.
A kacokaf abun da nake son nunawa anan shi ne, daukar matakai na kiyaye alakar yaro da yin abota da kowa (a yara) yana iya rage yiwuwar koyon dabi’un banza. Kodayake, iyaye ba su damu da wannan ba, sai dai idan sun ga dansu da wata bahaguwar dabi’a sai su fara mamakin inda ya koya.


Advertisement
Click to comment

labarai