Connect with us

LABARAI

An Kori Dan Sandan Da Ya Kashe ’Yar Hidimar Kasa

Published

on


Shalkwatan Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya (FCT) Abuja, da cafke wani jami’inta na dan sanda da kuma korar sa daga aiki a bisa zargin sa da kashe wata ‘yar bautar kasa (NYSC), Miss Angela Igwetu.
An yi zargin jami’in dan sandan mai mukamin Insifekta mai suna Benjamin Peter ya dambara wa Angela Igwetu alburushi ne a ranar Laraba a daidai Ceddi Plaza da ke birnin tarayya Abuja.
Jim kadan bayan da dan sandan ya mata ruwan harsashi mai rai, an garzaya da ita asibiti rai-kwaikwai mutu kwaikwai inda daga bisani kuma rai ya yi halinsa a lokacin da likitoci suke kokarin ceto rayuwarta a sakamakon harbin dan sandan.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Sadik Bello, ya shaida wa ‘yan jarida a ranar Juma’a kan cewar dakatar da jami’in nasu na zama tilas idan aka yi la’akari da laifin da ake zargin dan sandan nasu mai mukamin Insifekto da aikatawa, ya kuma shaida hakan a cikin ka’idojin ladaftarwa da hukunta masu kauce wa ka’idar aikin. Ya kara da cewa, wanda ake zargin za kuma su gurfanar da shi a gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da laifinsa, yana mai shaida cewar kawo yanzu kuma yana gargame a hanunsu.
Ya ce; “Shi (wanda muke zargi) tuni mun koreshi a aikin dan sandan, gabanin ma mu kai ga gurfanar da shi a gaban kotu, yanzu haka yana tsare yana jiran shari’a.
“An yi zargin ita yarinyar Angela Igwetu dan sandan ya harbeta ne a lokacin da take kururuwar neman ceto a cikin wata mota Toyota Camry inda take shelanta cewar an yi garkuwa da ita ne,” In ji shi.
CP Bello ya bayyana cewar tsohon dan sandan ya yi ikirarin cewar ya harbeta ne a lokacin da ke kokarinsa na harbin tayar motar domin tsaida motar, ya kai ga samun wacce tsautsayin ya rufta mata ne a lokacin da ya bude wa motar wuta.
Kwamishinan ya bayyana cewar rundunarsu bata baiwa wani jami’inta izinin aikata wani aikin da ya jibinci ta’addanci ba, don haka ne ya bayanna cewar ba za su lamunci hakan ba.
Kwamishinan sai ya yi ikirarin cewar za su tabbatar da adalci wa wanda tsautsayin ya rutsa mata ba tare da la’akari da jami’insu ne ya aikata laifin ba.
A wata zancen makamancin wannan, rundunar ‘yan sandan FCT ta yi alkawarin gudanar da bincike kan kisan da wani dan sandan ya yi wa wata ‘yar bautar kasa a ranar Laraba a Abuja.
Kakakin rundunar ta Abuja, DSP Anjuguri Manza ya shaida hakan wa kamfanin dillacin labarai a ranar Alhamis a Abuja.
Kamar yadda bayanai suka nuna, biyo bayan harbin ‘yar bautar kasan wato Igwetu an garzaya da ita zuwa asibitin Garki da ke Abuja daga bisani kuma rai ya yi halinsa.
Haka kuma, wani bincike ya nuna cewar jami’an asibitin sun ki amince da fara kula wacce aka harban matukar basu samu bayanin ‘yan sanda kan lamabarin ba, inda kuma jami’an asibitin suka musanta wannan zancen kai tsaye.
Ita dai ‘yar Bautar kasar kwana guda ya rage mata ta kammala yi wa kasa bauta dan sandan ya harbeta har lahira.


Advertisement
Click to comment

labarai