Connect with us

SIYASA

An Gudanar da Taron IMAN Na Kasa Karo Na 19 A Kebbi

Published

on


Kungiyar Islamic medical ta kasa ta gudanar da taron tan a jahohi 36 na kasar nan karo na goma sha tara a garin Birnin-kebbi a jiya. Taron ya gudana ne a dakin taro na kwalejin kimiya da fasaha da kuma kere-kere ta gwamnatin tarayya da ke a Birnin-kebbi, inda mambobbin kungiyar tare da shuwagabannin sun a kasa da kuma na jahohin kasar nan zasu tattauna kan al’amurran kungiyar da kuma tattaunawa kan matsalar marasa lafiya kan cutar ciwon sankara na mata da kuma maza da ke zama barazana ga rayuwar al’umma a kasar nan . Hakazalika kuma za’a tattauna game da matsalar shaye-shaye tsakanin matasan da kuma ‘yan mata na kasar nan.
Saboda haka shuwagabannin na kasa sun gyato ferfesa Abdulmuminu H. Rafindadi kuma tsohon shugaban jami’ar tarayya ta Lokoja domin gabatar da kasida mai taken “ matsalar cutar nan ta ciwon sankara da kuma yadda za’a shawo kan magance cutar a kasar Najeriya” watau a turance “ Cancer burden and prebention strategies in Nigeria”.
Haka kuma a cikin kasidar da ya gabatar a wurin taron karo na goma sha tara a jihar ta kebbi ferfesan Rafindadi yace “ mutanen dubu 72 ne ke mutuwa a kowace shekara a kasar Najeriya kan cutar nan ta sankara da ake cewa “Cancer “ , saboda da rashin kayan aiki kama tun daga rashin tsayayar wutar lantarki, magungunna da kuma na’urori na zamani domim yiwa masu fama da matsalar aikin da kuma kula dasu ta yadda yadace”. Haka kuma ya ci gaba da cewa asibitoti goma ne kawai ke duba masu fama da matsalar cutar nan ta ciwon sankara a kasar Najeriya wanda basu isar marasa lafiyan , domin ko wadannan asibitotin na fama da rashin kayan aiki na zamani.
Har ilayu ferfesa Abdulmuminu H. Rafindadi ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, hukumomin da abin yashafa da kuma gwamnatotin kasar nan da su taimaka wurin ganin an bada kyakyawar kulawa ga mutanen da ke fama da wannan matsalar cutar nan ta kansa na kasar nan.
Ya yi da shima shugaban na kungiyar ta Islamic medical na kasa Dakta Salisu Ismail ya bayyana cewa kungiyar tasu na taimakawa gajiyayu da marasa galihu musamman ‘yan gudun hijira, marayu da kuma talakawa masu rashin lafiya da basu iya biyan kudaden magunguna a yayi da suke asibiti. Ya kuma kara da cewa kungiyar na taimakawa yayi gudanar da aikin maniyata zuwa hajji.
Bugu da kari shugaban na kasa ya yabawa shuwagabannin kungiyar reshin jihar kebbi kan irin ayyukkan kiyon lafiya a kyauta da suka bayar ga mutanen jihar ta kebbi , inda yayi kira ga sauran shuwagabannin sauran jahohin nasu bi sawun takwarar su ta jihar kebbi domin yin irin abin da shuwugabannin na jihar kebbi keyi domin suma su kawo ma kungiyar ci gaba da kuma sunanta ga idon duniya
Shi ma shugaban na reshin jihar kebbi , Dakta Garba Umar Kangiwa ya godewa shuwagabannin na kasa da kuma gwamnatin jihar kebbi kan goyon bayan da yake samu daga garesu da kuma mambobbin kungiyar na jihar ta kebbi. Ya ci gaba da bayyanawa mahalarta taron irin nasarorin da kungiyar ta samu a jihar ta kebbi yasa shuwagabannin kungiyar na kasa suka yabawa reshin jihara ta kebbi , yace” daya daga cikin nasarorin da suka samu shine ayyyukkan bada da kiyon lafiya da kuma magunguna a kyauta ga mutanen karkara marasa lafiya iri daban daban a kananan hukumomi ashirin da daya na jihar ta kebbi”.
Daga karshe yagodewa dukkan wadanda suka halarci taron da kuma wadanda na taimaka wurin ganin cewa wannan taron na kungiyar Islamic medical karo na goma sha tara ya samu nasara a jihar ta kebbi muna godiya.


Advertisement
Click to comment

labarai