Connect with us

LABARAI

6 Ga Watan Yuli: Tunawa Da Bukin Ranar Soja Ta Kasa

Published

on


A ranar 6 ga watan Yuli 2018, rundunar sojojin Nijeriya na bikin zagayowar ranar soja ta kasa na wannan shekarar (NADCEL 2018) a garin Monguno ta jihar Borno. Bikin na wannan shekarar ya banban dana sauran na shekarun baya inda ake gudanar da rawar sojoji da baje kolin makamai, sau da dama kuma a na gudanar da bikin ne a filin Eagle Skuare dake Abuja ko kuma wasu daga cikin manyan biranen kasar nan. Wannan ba aka shi ne irin tsari da yadda ake gudanar da harkokin sojoji ba a karkashin mulkin shugaban sojojin Nijeriya (COAS) Laftanar Janar TY Buratai, shaharraren soja wanda ya yi suna a duniya wajen jagorancin yaki da ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda a kasarmu Nijeriya.
A bin daya banbanta bikin ranar sojoji na wannan shekarar dana sauran shekaru, musamman tun da aka kirkiro bikin shekara 155 da suka wuce, shi ne a wannan shekarar a nan yin wannan bikin ne a jihar Borno, a bangaren Arewa maso gashin kasar nan. A ‘yan shekarun baya babu wanda zai yi tunanin kawo ziyara garin Maiduguri ballantana garin Monguno don yin wasu harkokin da suka shafi bukukuwa na rayuwar jama’a. bugu da kari rundunar sojojin Nijeriya tana fuskantar sabbin kirkire kirkire da ci gaban zamani na bunkasar kayan aikinta da suka shafi makamai da sayran ci gaba a fannonin rayuwar bil’adam. Wannan bai zama abun mamaki bad a taken bikin na wannan shekarar ya zama “The Nigerian Army and National Security: A Panacea for Nigeria’s Economic Debelopment”. Kamar dai yadda shugaban rundunar sojojin Nijeriya ya bayyana a taron da ya yi da manema labarai ranar 29th ga watan Yuni 2018, inda ya ce, a halin yanzu rundunar sojoji sun shirya tsaf fiye da wani lokaci na bayar da gudummawarsu don kawo ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasar nan.
Taken na wannan shekarar ya kuma yi daidai da burinsa na ganin an samu “Kwararren soja kuma mai mutunci mai gudanar da aiyukansa kamar yadda tsarin mulkin kasar nan ya tanadar masa” wadannan kuma suna jigo a dalilin gaggarumin nasarar da rundunar sojan Nijeriya ta samu a shekara 3 da suka wuce.
Shawarar gudanar da bikin wanna shekarar a wannan bangare na kasar nan a bin a yaba ne kwarai da gaske, baya ga ba sojojinmu kwarin gwiwa da kuma jin cewa, lallai a na tare dasu, hakan kuma yana bayar da gaggarumin sanarwa cewar, lallai karshen kungiyar nan ta ‘yan ta’addan Boko Haram yazo karshe a kasarmu Nijeriya. Hakan kuma yana nuna cewar, an samu dawo da zaman lafiya da cikakken tsaro a yakin daya matsalar rashin tsaro na fiye da shekara 9 abin da kuma zai bude kofofin harkokin zamantakewa dana tattalin arziki, wannan kuma zai yi matukar bayar da gudummawa ga bunkasar kasar nan. A saboda haka, ya kamata dukkan hafsoshi da dakaru rundunar sojojin Nijeriya suyi alfahari tare da godiya na kasancewa a cikin rundunar sojojin Nijeriya a dai dai wannan lokacin da ake kaddamar da wani muhimmin lamari a tarihin sojojin Nijeriya. Babbar nasarar yaki tare da murkushe ta’addaci ta ‘yan ta’adda da kuma cikkaken kwarewa a aikin soja a cikin shekara 3 da Janar TY Buratai ya yi jagorancin rundunar sojojin kasar nan wani abin dab a a taba tunanin faruwarsa bane a shekarun baya.
A saboda haka ina amfani da wannan dama don in yi addu’a mazaje jajirtattatun sojojinmu hafsoshi da dakarumu da suka rasa rayukansu da wadanda suka ji raunuka a kokarin kare kasarmu a yanzu da kuma shekarun da suka gabata. Wannan sadakauwar ba zai tafi a banza ba. Muna addu’ar Allah Ya gaggauta ba wadanda suka ji raunuka lafiya. Ina kuma taya abokan aiki na murnar, abokai na a rundunar sojojin Nijeriya wadanda tsananin kishin kasarmu Nijeriya ya santa a shirye suke su mika rayuwarsu don kare mutumci da martar Nijeriyada suka, suna shirye su bayar da rayuwarsu saboda wannan kasar tamu Nijeriya. Muna kuma mika gaisuka ga mata da yara da sauran iyalan hafsoshi da dakarun sojojin Nijeriya a bisa soyaya da taimakawa da kiuma karfafawa da addu’o’insu da kuma fahimtarsu ga rudunar sojojin Nijeriya.
Ina kira ga daukacin ‘yan Nijeriya dasu hada hannu da rundunar sojojin Nijeriya wajen wannan gaggarumin biki na ranar sojojin Nijeriya na wanna shekarar (2018) musamman ganin yadda suka daukaki tare da kare sunan kasar nan a idon duniya. Sojan Nijeriya bashi da na biyu a wajen dauriya da jajircewa da tsayuwa wajen aiki da kuma kishin kasa haka kuma sojan Nijeriya ya yi fice wajen son zaman lafiya da mutunta bil’adam.
Muna matukar godiya gareku a kokarinku na shiga inda duk wani mai raina tsoron shiga kuka kuma yi nasara a kan makiyan Nijeriya. Gudummawarku da kokarinku na jure duk halin da kuka samu kanku tare da barin iyalanku don ku fuskanci fagen fama saboda Nijeriya dama duniya gaba daya ta samu zaman lafiya tare da samun ‘yanci ya sanya kun zama na musamman, suna da mutuncin da kuka kawo wa Nijerya ta hanyar wadanna aiyyuka naku zai ci gaba da zama abin ambato a zukatan ‘yan Nieriya.
Ina taya hafsoshinmu da dukkan dakarunmu a duk inda suke, cikin Nijeriya ko kasashen waje murnar bikin ranar sojoji ta kasa (Nigerian Army Day). Allah Ya Yi muku albarka gaba daya
Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, ya rubuto wannan mukala ne daga garin Jos, Jihar Filato.


Advertisement
Click to comment

labarai