Connect with us

SIYASA

2019: Wata Kungiya Ta Bayyana Goyon Baya Ga Kwankwaso

Published

on


Wata Kungiya mai suna Kwankwasiyya Frontiers (KF) ta yi kira ga yan Nijeriya da su zabi tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin shugaban kasa a zaben kakar 2019, inda suka ce Kwankwaso ne daya tilo da zai iya kai kasar tudun mun tsira.
Shugaban kungiyar reshen jihar Ribas Mista Ogonna Oriekie ne ya bayyana hakan a garin Fatakwal lokacin kaddamar da kungiyar reshen jihar, inda kuma ya shawarci yan Nijeriya da su cire bambancin addini ko na addini a gefe don marawa Kwankwaso baya.
Oriekie ya ci gaba da cewa lokacin da Kwankwaso ya yi gwamnan jihar Kano ya inganta tattalin arzikin jihar da sadaukar da kai wajen inganta rayuwar yan jihar, musamman tabbatar da gaskiya da rikon amana da adalci.
Da yake kaddamar da kungiyar, wanda ya kafa ta reshen jihar Fasto Hilary Chukwuma, ya yi kira da samar da hadin kai a tsakanin magoya bayan kungiyar, ya kara da cewa sai inda hadin kai ne, za a ci gaba.
A karshe ya yaba wa magoya bayan kungiyar saboda yin amanna da akidojin siyasar Kwankwaso da kuma nuna goyon bayan su.


Advertisement
Click to comment

labarai