Connect with us

KASUWANCI

Zuba Market: Kasuwar Da Ta Shahara A Sayar Da Kayan Marmari

Published

on


Gabatarwa
Jaridar Leadership A YAU ASABAR ta yi tattaki zuwa shahararriyar kasuwar kayan marmari ta garin Zuba da ke yankin Abuja, cikin karamar hukumar Suleja ta jihar Neja, in da ta sadu da daya daga cikin tsofaffin mambobin kungiyar wannan kasuwa, wanda kuma bisa amincewar shugaban kasuwar Alhaji Shafi’u Yahaya, Sabo Ahmad Kafin-Maiayaki, ya zanta da shi. Wanda ya bayyana tarihin kasuwar da nasarorinta da matsalolin da suke damunta da kuma kiransa ga gwamnati kan bukatar tallafa wa kasuwar, sannan kuma ya bayyana nasarorin da shugaban kasuwar, Alhaji Shafi’u Yahaya ya samu daga zabarsa zuwa wannan lokaci. Ga kuma yadda ya bayyana wadannan abubuwa daki-daki. Kafin nan ya fara da gabatar da kansa ga masu karatunmu, wanda ya ce; Sunansa Ibrahim Muhammad Talba, babban dila ne mai saye da sayar da kayan marmari a wannan kasuwa ta Zuba, kuma yana daga cikin wadanda aka kafa wannan kasuwa tare da su.

Tarihin Kasuwar Kayan Marmari Ta Zuba
Tarihin wannan kasuwa ya faro tun kimanin shekara ashirin da daya zuwa ashirin da biyu ta suka wuce watau, wajajen karshen lokacin mulkin marigayi Sani Abaca, wanda a lokacin muna Wuse, daga nan aka tashe mu zuwa New-Market, muka ci gaba da kasuwanci, a nan ma aka ce mu tashi mu koma Zuba. A gaskiya a wannan lokacin abin bai yi mana dadi ba. Domin muna ganin tashinmu daga wannan kasuwa da ke cikin gari zuwa nesa da gari, zai kawo mana koma bayan kasuwancinmu.Da yake a lokacin muna da kungiya karkashin jagorancin Alhaji Amadu Sanadi.
Haka dai wasu daga cikinmu suka daure muka dawo Zuba, yayin da wasu suka koma Dei-Dei wasu Marabar Nyanya, da sauran wasu wuren, suka ci gaba da kasuwancinsu, saboda sun yanke kaunar cewa, kasuwancinsu ba zai ci gaba da habaka ba, a wannan kasuwa da suke ganinta a nesa da gari.
Akwai wani dattijo, wanda yake uba ne a wannan kasuwa, ana kiransa Alhaji Ado Kofa, shi ne ya zo ya share filin wannan kasuwa, ya jagoranci kafa ta,har aka fara zuwa kadan-kadan, sannan ya yi kokarin karfafa dangantaka tsakanin ‘yan kasuwar da ‘yan asalin wannan gari na Zuba. Haka ya taimaka kwarai wajen samun cikakken goyon baya daga gare su, sai kuma ya nemi gwamnati ta tabbatar masa da wannan kasuwa. Cikin ikon Allah kuma ya samu wannan sa’ar, gwamnati ta bbatar masa da ita. Daga nan kasuwar ta ci gaba da habaka.
Bayan rasuwar Alhaji Ado Kofa, sai kuma wani daga cikin dattawan kasuwar kuma shi ma uba a kungiyar masu sayar da kayan marmari, Malam Yahaya, ya ci gaba da tafiyar da wannan kasuwa, cikin ikon Allah shi ma bai wuce shekara daya zuwa daya da rabi ba ya rasu.
Sannan sai kuma Labaran Abubakar ya ci gaba da rike wannan kasuwa har na tsawon shekara tara, wanda kuma a halin yanzu yana nan a matsayin uba a wannan kasuwa, yana ci gaba da bayar da gdummawa ta hanyar shawarwari da kuma daidaita al’amura.
Bayan saukarsa, Nura Haruna, wanda shi kuma ya shafe shekara hudu yana gudanar da mulkin wannan kasuwa. Bayan da ya cika shekara hudun ne ya sake neman zango na biyu, amma cikin ikon Allah sai jama’a suka yanke hukuncin zabar shafi’u Muhammad, wanda kuma a halin yanzu shi ne shugaban wannan kasuwa ta sayar da kayan marmari da ke Zuba.

Abubuwan Da Ake Saye Da Sayarwa A kasuwar.
Abu ne mai wahalar gaske mutum ya iya fadar abubuwan da ake kawo wa wannan kasuwa duka domin sayarwa, duk da cewa, kasuwar ta yi fice a kan sayar da kayan marmari, to amma ko a kayan marmarin da wuya a iya gane yawan nau’o’insu.
Saboda haka daga cikin kayan marmarin da aka fi saninsu a wannan kasuwa su ne:
Lemo: Lemo shi ne ya debi kaso ma fi yawa a wannan kasuwa, shi ya sa ma wasu kan kira kasuwar da kasuwar ‘yan lemo. Saboda lemo shi ne tubalin da aka yi amfani da shi wajen kafa wannan kasuwa. Ana kawo lemo daga kasahen Yarabawa, irinsu Oyo da ogun da ondo da kuma kasashen Binuwai da sauransu. Wani lokacin ma har daga wajen kasar nan ana kawo lemo wannan kasuwa.
Kankana: Ita kuma kamar yadda aka sani kankana ana kawo ta ne daga Arewa. Ana kawo ta daga jihar Kano da Jigawa da Maiduguri da Bauchi da Sakkwato da Birnin Kebbi da Katsina da Neja. Wadannan wurare ne da ke kawo kankanarsu wannan kasuwa da yawa.
Filanten: Ita kuma filaten a kan kawo ta daga Bayelsa da kasashen Yarabawa da kuma ‘yar kasar nan ta Abuja, wadda ake kira gwari filanten, saboda daga wadannan yankuna aka fi samun ma fi yawan filanten din da ake sayarwa a wannan kasuwa. Haka kuma a kan kawo ta daga Kamaru
Ayaba: Ita ma ana kawo ta daga kuros Riba da kasar Yarabawa, saboda haka wadannan wurare ke bayar da gudummawa ma fi yawa wajen samar da ayaba.
Abarba: Ita kuma ta fi fito wa daga yankin Bendel, haka kuma ana kawo ta daga kasashen waje irin su Kwatano da sauransu, da kuma kasashen Yarabawa, amma dai Bendel ita ta fi kowane yanki samar da abarba a wannan kasuwa.
Gwanda: Gwanda na fito wa daga yankin Bendel da Auchi, sannan akwai irin ‘yar kasa ta gwarawa wadda suke kawo wa, amma dai ba ta da yawa. Saboda haka in dai maganar gwanda ce yankin Bendel su ne kan gaba wajen samar da ita.
Tanjalo da Tanderu da Agwaluma: Wadannan ‘ya’yan itace da wasu makamantansu an fi samunsu daga kasar Yarabawa.
Mangwaro: Mangwaro ita ma ana kawo ta daga Binuwai da kuma ‘yan kasa, wadda ake samunta a yakin Abuja da Neja.
Kwakwa: Kwakwa an fi samunta daga Badagir.
Gudummawar Kasuwar Wajen Samar Da Aikin Yi
Wannan kasuwa, kasuwa ce da Allah ya albarkace ta da dimbin jama’a daga kowane yanki na kasar nan wadanda ke saye da sayarwa. Saboda akwai kuma wasu mutanen da suke yi wa masu saye da sayarwar hidima wadanda su ma kasancewar kasuwar na ci gaba da gudana a wannan wurin ne suke zau ne kuma suke samin abin biyan bukata. Irin wannan rukunin jama’a wadanda suka samu aikin yi wannan kasuwa sun hada da, ‘yan dako da ‘yan okada da masu sayar da abinci da ‘yan sintiri da direbobi da sauran masu sayar da kayan amfani. Saboda haka samar da aikin yi a wannan kasuwa bai tsaya kawai a kan wadanda ke saye da sayarwa ba kawai. Don haka wannan kasuwa na bayar da gagarumar gudummawa wajen samar da aikin yi a kasar nan.

Gudummawar Kungiya Ga Mambobinta
Kasancewa wannan kasuwa na karkashin kungiya ne yadda ake tafiya cikin hadin kai da fahimtar juna da kuma taimaka wa juna wajen samun ci gaban rayuta tare da kare hakkin dukkan mamaban wannan kungiya.
Babu shakka shugabancin wannan kungiya na kokarin tallafa wa mambobinta a kan dukkan wani abu da ya same su tafuskar kyautata musu. Idan kuma abin ya fi karfin wannan kungiya muna da babbar kungiya ta kasa ita ma tana shigo wa domin taimaka wa mambobi.
Wani abin jin dadi shi ne da yawa daga mambobinmu da suka kuma ske ta sha’awar yin aikin gwamnati, an taimaka musu sun samu aiki, sannan akwai wadanda aka taimaka musu wajen samun aikin dan sanda da kuma tallafa wa iyalai musammam wajen fuskara ilimin ‘ya’yansu.

Shugabancin Wannan Kasuwa.
Cikin ikon Allah tunda aka kafa wannan kasuwar ta yi dacen shugabanni dattawa, wadanda kullum kokarinsu shi ne ya ya za a yi wannan kasuwa ta ci gaba. Bisa kokarin da suka dade suna yi da taimakon Allah ya sa aka samu ci gaban da ake gani a halin yanzu.
Idan muka dawo batun shugabancin kasuwar a wannan lokaci wadda ke karkashin jagorancin Shafi’u Muhammad, sai mu ce Alhamdu Lillahi shi ma ya bi sahu, ya ci gaba da dora wa inda magabata suka tsaya. Shafi’u Yahaya shugaba ne da jama’a ke kaunarsa, shi ma kuma yake kaunarsu. Saboda haka ko da aka zo zabe al’ummar wannan kasuwa suka bayyana ra’ayinsu na zabensa kuma suka samu gamsuwa lokacin da ya samu nasara.
Da yake masu hikimar magana na cewa, “halin mutum jarinsa” saukin kan Shafi’u Yahaya ke da shi ya ba shi dama wajen sanin halin da al’ummar wannan kasuwa ke ciki, domin kuwa duk lokacin da bukatar ganisa ta taso za a gan shi ba tare da wata matsala ba. Saboda haka al’umma ke samun nutsuwa wajen zuwa su bayyana dukkan abin da ya dame su, sannan shi kuma yakan samu damar jin halin da ake ciki ya kuma samar da mafita.

Kira Ga gwamnati
Kirana ga gwamnatin kan wannan kasuwa shi ne akwai abubuwa da yawa da kasuwar ke bukata, wadanda idan an yi su zai taimaka wajen bunkasata, sannan kuma a samu damar gudanar da kasuwanci cikin walwala. Saboda haka, babbar shawarata ga gwamnati ita ce ta lura da cewa me jama’a suke bukata wanda shi ne zai taimake su, ba wai abin da ita gwamnatin ko kuma wadanda ma ba ‘yan kasuwa ba suke ganin shi ne ya kamata a yi wa ‘yan kasuwar.
Saboda haka kamar a wannan kasuwa za ka ga ana bukatar ciko da samar da hanyoyin magudanan ruwa da kuma gina manyan rumfuna da shaguna.


Advertisement
Click to comment

labarai