Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Umurci A Sake Zaben Jam’iyyar APC Na Jihar Imo

Published

on


Babbar kotun tarayya da ke zama a Owerri a jihar Imo ta bayar da umurnin a sake gudanar da zaben Gundumomi da na kananan hukumomi na jam’iyyar APC a jihar ta Imo.
Da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, Alkali Lewis Allagoa ya ayyana cewar jam’iyyar APC ba ta gudanar da wani zabe a jihar ba a cikin watan Mayun da ta gabata.
Jam’’iyyar dai ta samu kanta a cikin mawuyacin hali na rikicin cikin gida a jihar a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar tun bayan zaben da wasu bangare suka yi ikirarin gudanarwa a jihar.
Alkali Allagoa ya bayar da umunin dai a sake gudanar da zaben babban jam’iyyar domin wanzar da zaman lafiya, adalci, da kuma tabbatar da cikkakken demoradiyya a jihar, ya ce hakki ne a tabbatar da kare demokradiyya da tabbatar da adalci da ‘yancin mambobin jam’iyya dangane da wannan zaben, don haka ne ya ce dole ne kawai a sake zaben.


Advertisement
Click to comment

labarai