Connect with us

MAKALAR YAU

Harkar Ilimi: Ina Kwalejojin Horar Da Malam Ne?

Published

on


Akwai Karin maganar Hausawa da ke cewa ‘kowa ya tuna bara, to bai ji dadin bana ba.’ Na kawo wannan Karin Magana ne saboda batun da nake son in yi Magana a kai, wanda ya shafi harkar ilimi a kasar nan, musamman a nan Arewaci.
A kwanakin baya na kawo bayanin yadda Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki damarar ganin ta dawo wa da harkar ilimi martabar da ya kamata a ce tana da ita, duk da yake wannan yunkuri ya fukanci wasu ’yan matsaloli masu nasaba da siyasa.
Wannan al’amari haka yake, musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu bangarorin ilmi suka durkushe, saboda bugun zauna ka-ci Doyar da aka yi masu, shi ya sa aka shiga wannan halin da ake ciki da dadewa.
Wannan ya sa ake ta samun koma-baya, musamman ma a Makarantun Firame, wadanda ake ganin su ne babban ginshikan ilmi ga ‘yan makaranta, ba ma kamar tun suna kanana saboda abubuwa sun fi saurin shiga kwakalwarsu. Idan haka ta faro daga Firamare to ashe ke nan an yi baya ba zane, domin komai daga Firamare ake fara shi, da zarar kuma an samu matsala daga can, to shi ke nan tafiya ta tafi sai dai a yi ta gura-gura.
Idan har aka fara samun matsala daga can, to ai kuma shi ke nan , sai dai a ce Allah ya kiyaye. Idan kuma aka waiwaya baya, yadda al’amuran suke shekarun baya, lokacin da akwai Makarantun koyon sana’a, wadanda aka fi sani da ‘Technical schools,’ sai kuma ‘Commercial Colleges’ na harkar kasuwanci, sai kuma babbar Yaya daga cikinsu, wato ‘Teachers Colleges’ da ake kira kwalejojin horon Malamai.
Tuni tun ma kafin a fara shiga wannan harkar kulle kurciya ta bangaren ilmi, saboda idan muka duba kamar yadda aka bankado irin abubuwan da ke faruwa, a Makarantun Firamare na jihar Kaduna, ai abin sai dai a ce a yi sha’ani, wai an cuci na kauye. Saboda hakan ai kamar gidan kowa da akwai ne, idan aka dan yi shiru nan gaba, za a iya samun Jihohin da suka fi Kaduna.
Da farko dai idan dalibi yana Form 2 (aji biyu) yana kusa ya shiga aji na uku, akwai wata jarabawa da ake yi mai suna ‘Aptitude Test,’ daga wannan jarabawar ce ake ware dalibai wadanda aka ga zai fi dacewa a ce sun tafi makarantun horon Malamai, wasu a kai su ‘Tehnical Schools,’ wasu kuma ‘Commercial Colleges,’ wasu kuma sai ‘Science Schools,’ na kimiyya, haka abin yake, wasu ko dai a bar su wannan makarantar ko kuma a mayar da su wasu makarantu abin da ake kira ‘Transfer.’
Bambancin da ke akwai shi ne, akwai wasu tun lokacin da ake masu ‘interbiew’ bayan ‘Common Entrance Edamination’, shugabannin ‘interbiew’ ke yanke shawarar su, kai su Makarantun Horon Malamai ko ta Maza ko mata, sai kuma Makarantun Koyon Sana’a, da kuma wasu Makarantun koyon kasuwanci.
Ire iren wadannan makarantun wadanda nake kiran su, na musamman saboda suna taka muhimmiyar rawa wajen samar wa kasa kwararrun Malamai, domin tun suna ‘yan yara ake koya masu, ilmin ya shiga cikin jikinsu, sun kuma saba domin abin da za ka yi shekaru biyar ana koya maka, da wanda zai yi ‘yan watanni, ko shekara daya zuwa uku ai da akwai bambanci.
A Arewacin Nijeriya aka yi irin wadannan makarantu. Da farko dai akwai ‘Katsina Teachers College.’ Wannan makaranta ta bada gudunmawa wajen samar da Malamai, a Arewacin kasar nan, muna iya daukar shugabannin siyasar farko na Nijeriya wadanda can suka yi Makaranta, tun ma ginin nata yana a na kasa, kamar su Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato, Sir Abubakar Tafawa Balewa , Malam Aminu Kano, Alhaji Umaru Sanda Ndayako Etsu Nupe, Alhaji Isa Kaita, Sir Kashim Ibrahim, da dai sauran mashuran mutane wadanda suka taba taka rawa wajen ciyar da kasar nan
Garabasar da ake samu a irin wadannan Makarantu na Horon Malami ba ta wuce yaro tun yana dan karami yake tashi da akidar koyarwa a zuciyar shi, an sa masa ita , a cikin hikima zai kuma tashi yana ganin muhimmanci da kuma girmamata, al’amarin aikin koyarwa, ya tashi yana alfahari da hakan. A tuna fa dalibi a lokacin shekaru biyar yake yi a Makarantar, ana koya ma shi yadda zai fuskanci aikin koyarwa, bayan ya kammala wani ya kan fara aikin koyarwa, kafin ya wuce abinda ake kira Adbance Teachers Colleges, nan kuma ya yi shekaru uku, bayan haka ya fito da takardar shedar NCE, daga nan kuma sai Jami’a inda zai karanta Bachelor of Education, to ko dai ba Agwada Ba, Ai Linzami Yafi Wuyan Zakara.
Yanzu abin da ke a kasa ta hanyar koyarawa shi ne sai dalibi ya kammala Sakantare, daga nan ya je zuwa College of Education idan mai sha’awar koyarwar ne, ya yi shekaru uku ya samu NCE. Ai idan aka ce da wanda ya bi tsarin irin na da , da kuma na yanzu su kama aikin koyarwa , ai wanda ya bi ta dogon zango dalibai zasu fi saurin fahimtar abubuan da yake koya masu.
Su kuma Makarantun Koyon sana’a, a Arewa akwai ‘Gobernment Technical Secondary Schools’ a jihar Katsina yanzu a Mashi cikin Karamar Hukumar Mashi da aka kirkirota daga jihar Katsina, ita kuma Jihar Katsina daga jihar Kaduna aka kirkiro ta. Sai kuma Soba a Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, da akwai kuma daya a Kano da ake kira da suna ‘Technical College,’ suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da kwararru.
Wani abin burgewa, irin daliban da suka yi wannan Makarantu tun a can ake koya masu sana’o’i daban-daban wadanda ko da ba su samu wucewa Makarantu ba, suna dai da sana’a a hannunsu ba sai sun jira gwamnati ta samar masu da ayyukan yi ba, su ma suna iya dogaro da kansu, har ma wasu su zo , wurinsu su koya.
Sana’o’in da ake koya ma dalibai a matsayin darussa sun hada da ‘Technical Drawing, Building, Woodwork, Metal work, Carpentary, Electrical da Electronic, Plumbing’ da dai sauran makamantansu. Ba dai sai na yi wani dogon bayani ba akan muhimmanci masu irin wadannan sana’o’in, a Nijeriya ba ma Arewa kadai ba, yanzu ashe dawo da ire-iren wadannan Makarantu na musamman ai ba karamin alheri ba ne a kasa, ba ma kamar halin da aka shiga yanzu na yadda gwamnatoci ba su iya samar wa wadanda suka kammala makarantu da ayyukan yi.
Yanzu da yake akwai Jami’o’in Kimiyya da Fasaha a Minna, Yola, Bauchi, Owerri, da dai sauran jihohi, irin daliban da suka yi Makarantun Koyon sana’a ai, su ga ya dace su je irin wadannan Jami’o’in na musamman, ga kuma Kwalejojin Koyon Fasaha wato Polytechnics wadanda har Hukuma ce mai kulawa da su ake da ita.
Ba wai ba a son bullowa da wasu sababbin tsare-tsare ba ko manufofi ba ne, abin a yi maraba da wannan tunani ne, abin ba haka yake ba, musamman ma a bangaren ilmi wanda shi ne ginshikin rayuwa. Matsalar ita ce, ba tare da, sai an bari an lura da yadda shi sabon tsarin zai iya kasancewa ba, abin ban takaici shi ne, tsohon ake wulakantawa a yi watsi da shi.
Muna iya duba lokacin da aka bullo da Makarantun Jeka-Ka-dawo da aka fi sani da ‘Day Schools,’ wanda aka fake da matsalar kudi ce ta sa haka fito da su, to ai kowa ya ga ci-bayan da aka yi maimakon ci gaba, lokacin da aka bullo da Makarantun. Ta bangaren tarbiyyar da ake koya a irin wadannan Makarantun Kwana da kuma shi irin ilmin da ake samu a can ba, ai bai ma kamata a ce a hada su ba. Kowa yana iya tunawa da yanzu an samu faduwar darajar ilmi tun daga wancan lokacin.
Yanzu dai Dabara Ta Ragewa Mai Shiga Rijiya. Wasu daga cikin wadanda suka tsinci kansu a harkar Koyarwa ba son abin suke ba har ga zucci, suna dai yi ne, domin sun rasa ayyukan da suke son yi, ko kuma fannin da suka karanta maganar gaskiya ke nan ‘Sai An Sake Yi Wa Tufkar Hanci’ idan har ana son a dawo da martabar da kuma darajar da ilmi yake da ita, a kuma samu ci gaban al’umma da kuma kasa.


Advertisement
Click to comment

labarai