Connect with us

LABARAI

Duk Mai Jin Shi Tsarkakakke Ne A APC, PDP Ta Shayar Da Shi Mama Sule Lamido

Published

on


Dan takarar Shugaban kasa, a Jam’iyyar PDP, tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa, duk mai jin shi tsarkakakke ne a jam’iyar APC, a kasar nan, jam’iyyar PDP ce ta shayar da shi mama. Dan takarar ya bayyana haka ne a lokacin da yake bude ofisin kamfen dinsa na Jihar Zamfara, a Gusau Babban birnin jihar Zamfara .
Dan takarar ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammad Buhari shi ma’asumi ne ya zo ne don ya yi wa barayi ‘yan PDP, hisabi ,wanda bai koma APC ba. Na san cewa shugaban kasa ba ya sata amma barayin gwanoni,na sata kuma su kai masa ya amsa, don haka ya nemi jin hukuncin mai amsar kudadan sata ga mahalarta taron.
Ya kuma bayyana cewa tsahon gwamna jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya sha bayyana cewa, lokacin da suna ANPP, gwamnoni na satar kudi, su kai wa Muhammad Buhari, ya yi kamfen da su.
Saboda haka, duk wani mai tinkaho da mulkin a cikin jam’iyar APC yanzu kuma, mai jin kansa shi tsarkakake ne na fada na kara fada cewa ‘ PDP ta shayar da shi har ya kawo lokacin da zai a uwarsa butulci.
Dantakarar ya sha alwashin idan jam’iyar PDP ta zabe shi a matsayin dantakararta na shugaban kasa, zai mai da hankali wajen. Samarwa Matasa abin yi, abin takaici shi ne, yau gamu da matasa sun gama digiri babu aikin yi, sai bangar siyasa, su kuma masu mukaman siyasa yaransu na waje suna karatu. Da yardar Allah idan muka kai gaci wannan matsalar sai labari.
Sannan ya kara da cewa ‘ zai mai da hankali wajen farfado da tatalin arzikin kasa, da kuma magance matsalar tsaro da ta da baibaye wannan kasa ta mu.
Karshe kuma ya yi kira ga ‘yan jam’iyar PDP, da su maramasa baya wajen ganin ya zamo dantakararsu na shugaban kasa a zabe na shekara ta 2019.
A na sa jawabin shugaban jam’iyar PDP, na jihar Zamfara, Sanata Hassan Nasiha ya bayyana jin dadinsa da ziyar dan takarar shugaban kasar kuma ya tabbatar masa da cewa ‘ PDP a jihar Zamfara kanta hade yake kuma za su yi iyaka kokarinsu na ganin an kara samun ci gaba da kuma ba dan takarar cikakke goyan baya.
Shi kuwa sakataren jam’iyyar na jihar, Honarabul IIbrahim Umar Dangaladiman Birnin-magaji ya bayyana godiyarsa ga dubun-dubatar ‘yan jam’iyyar PDP, da suka taryi dan takarar cikin kwanciyar hankali da luma.


Advertisement
Click to comment

labarai