Connect with us

LABARAI

Balarabe Musa Ya Soki Yunkurin Kirkiro ‘Yan Sandan Jihohi

Published

on


Tsohon gwamanan tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya sanar da cewar kirkiro da ‘yan sandan jiha ba zai magance kalubalen rashin tsaro da ke addabar Nijeriya ba a yanzu.
A hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa, a jihar Legas ranar Laraba. Musa yana mayar da martani ne a kan matsayar da majalisar dattawa ta yanke na yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan kwaskwarima a zaman da majalisar ta yi ranar Talata, inda majalisar ta umarci kwamitin majalisar a kan yi wa kundin tsarin mulkin garambawul yadda za a bayar da damar kirkiro da ‘yan sanda na jahohi a kasar.
Balarabe ya yi nuni da cewar kirkirowar ba zai haifar wa da kasar nan da mai ido ba, kuma hakan ba abin da zai warkar, amma na yi amannar cewar, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta kara karfafa aikin ‘yan sanda shi ne kawai mafita.
Ya ci gaba da cewa, muna fuskantar matsalar ce saboda rashin bai wa ‘yan sandan isasshen horon da ya dace da kuma samar masu da ingantattun kayan aiki, saboda haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara horas da su a kan sanin makamar aiki da tanadar masu da makamai da kuma kara daukar ‘yan sanda aiki.
Ya yi nuni da cewar, wasu gwamnnonin jihohin za su yi amfani da damar ce don kawai su cima ma wasu burinsu na siyasa, har ila yau, da aka tambaye shi ko gwamantin tayya za ta iya samar da isassun kudaden da za ta iya ci gaba da tafiyar da ‘yan sandan kasar nan, sai ya ce, abin ba maganar kudi ba ce,amma niyya mai kyau ta siyasa ita ce mafita.
Balarabe ya yi nuni da cewar harkar lamarin tsaro ta kowa da kowa ce ba ta mutum daya ba ce saboda haka ina kira ga daukacin ‘yan kasar nan da su bayar dá nasu goyon bayan don samar da cikakken tsaro a kasar nan.
Da kuma yake mayar da martani a kan furucin Tsohon ministan sufuri Ebenezer Babatope, na cewar kirkiro da ‘yan sanda na jiha zai magance rashin tsaro a kasar, tsohon gwamnan ya ce, tsohon ministan shaci fadi ne kawai yake yi.


Advertisement
Click to comment

labarai