Connect with us

LABARAI

Sarkin Bauchi Ya Gargadi Masu Rabon Tallafin Rage Radadin Ibtila’in Guguwa Su Yi Adalci

Published

on


Sarkin Bauchi Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu ya bukaci masu Gundumomi, masu unguwanni da kwamitocin da aka daura wa alhakin raba kayayyakin rage radadi ga wadanda ibtila’i Guguwa ta shafa a Bauchi da su gudanar da aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ke zantawa da ‘yan jarida a fadarsa, ya bayyana cewar kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da halin da wadanda aka samar da tallafin dominsu da kuma yanayin da suka samu kansu a ciki.

Haka kuma ya bayyana cewar a sakamakon korafe-korafen da ake samu daga wajen mutane musamman wadanda lamarin ta shafa ne ya sanya shi yin kiran ga wadanda aka daura wa alhakin kula da rabon domin tabbatar da adalci a tsakani.

Ya kuma yi kira ga kwamitin samar da kayyakin rage radadin da su yi aiki kafada-kafada da masu unguwanni domin fidda sahihan wadanda lamarin ta shafa don guje wa mika wa wadanda basu gamu da ibtila’in ba.

Mai martaban ya yi bayani bayanin cewar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku  Abubakar ya kawo tallafin miliyan 10, Gwamnatin Gombe miliyan goma da shinka da masara motar tilera daidai, hadi da alkakawarin miliyan 50 daga ma’aikatan matatar mai ta kasa NNPC, kamfanin saida kayyaki na Jifatu buhuhhunan masara 100.

Ta bakin mai martaba Sarkin Bauchi, “Babban manajan kamfanin mai na NNPC ya yi alkawarin tallafin da za su bayar naira miliyan 50, muna sauraro lokacin da za su turo, idan Allah ya sa sun turo ta hanunku sai a sanar da ni; idan kuma ya turo ta hanuna zan tura muku.

“Alhaji Atiku Abubakar ya zo ya jajanta ya bani Check na miliyan goma; akwai shi mai kasuwar Jifatu ya aiko da masara 5kg guda 100,” In ji Rilwanu Sulaiman.

Mai martaban ya bukaci dukkanin wadanda aka daura wa alhalin rabon su yi adalci su kaurace wa son rai ko son kai a lokacin da suke aikin raba tallafin ga wadanda ake bukatar hakan ya je garesu.

Da yake tofa albakacin bakinsa Sakataren kwamitin rabon Alhaji Kabiru Yusuf Kobi ya ce za su yi amfani da rahotonin da masu unguwani suka basu wajen rabon. Alhaji Kobi ya ce kwamitin za ta fara aiki ne a ranar Juma’a “Nan da ‘yan kwanaki kadan ma’aikatanmu za su shiga dukkanin yankunan da lamarin ta shafa, tun kafin ma’aikatan su zo mun rigaya mun daddale gidajen da lamarin ya shafa, za ka tsaya a jikin gidanka a dauke hoto a baka tallafinka,” In ji shi.

Daga bisani ya bukaci jama’a su basu hadin kai sosai wajen samun nasarar rabon.


Advertisement
Click to comment

labarai