Connect with us

LABARAI

Gwamna Ganduje Ya Yaba Wa Karuwar Ayyukan Gwamnatin Tarayya A Kano

Published

on


A kokarin da Gwamnatin Tarayya take yi na tabbatar da ci gaban Jihar Kano, Gwamna Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana farin cikinsa bisa gaggarumin aikin sabunta hanyar Kano, Kaduna zuwa Abuja da aka kaddamar a cikin mokon daya gabata, bayan nan kuma ga tallafin samar da ingantaccen ruwa a Jihar Kano domin kawo karshen matsalar ruwa a fadin Jihar Kano.

Gwamnan na wannan Jawabin ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta Jihar Kano da aka saba gudanarwa duk mako a fadar gwamnatin Jihar Kano, gwamna Ganduje ya bayyana cewar, muna matukar farin ciki da bayar da aikin gina haryar Kano, Kaduna zuwa Abuja da Gwamnatin tarayya ta ba Kamfanin Julius Berger akan kudi sama da Naira Biliyan 160.

Gwamnan Ganduje ya ce, a lokacin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Kano, daya daga cikin bukatun da muka gabatar masa  aciki harda sake ginin waccan hanyar mai muhimmancin gaske.  Gashi cikin yardar Allah Gwamnatin tarayya ta bayar da aikin wannan hanya a cikin makonnin da suka  gabata  wanda tuni aka fara gudanar da shi aikin.

A cewar Gwamna Ganduje wannan na nuna yadda tabbacin dattijantakar da shi Shugaban kasar mu keda ita, mun gabatar da bukata ta kuma an amsa bukatarmu, cikin kankanen lokaci, Ganduje ya ci gaba da cewar wannan kyakkyawar kulawar ke nuna tabbacin shugaban kasar na samar da ci gaban da ake bukata a Najeriya, wannan ya sa muke jadaddawa jama’a bukatar sake zabar Jamiyyar APC domin ci gaba da wadannan ayyukan na alhairi.

Don haka sai Gwamna Ganduje ya jinjinawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa samar da Dala Biliyon 475 daga Kasar Faransa, daga cikin wannan kudaden Jihar Kano ta samu Dala Miliyon 75 don inganta harkar ruwa a Jihar Kano, Gwamna Ganduje ya kara tabbatar da cewa wannan kyakkyawan ci gaba ne kuma hanya ce ta rubanya ayyukan ci gaba wanda ake fatan ya tarar da jama’a a matakai daban daban.

Da yake yiwa majalisa Jihar Georgia, Atlanta, United State Of America jawabi, Gwamna Ganduje ya bayyana aniyar Gwamnatinsa ta hada karfi da gwamnati Georgia da kuma Atlanta domin amfanar juna da abubuwan ci gaban al’ummar mu. Mun kuma kasance a wadannan garuruwa domin ganin yadda manyan birane ke bunkasa domin aro irin wannan ci gaba zuwa Jihar Kano. Muna sha’awar fahimtar hanyoyin kawar da yawan zirga zirga a manyan titunan mu da kuma yadda zamu yaki aikata manyan laifuka a tsakanin al’umma a cewar Gwamna Ganduje.

Wannan ziyarar ta taimaka mana wajen bukasa al’adunmu a tsakanin kasashen mu, ya ce na ziyarci  Sarakunan larduna City Union da kuma Fulton, wadanda suka amince da zuwa Jihar Kano domin halartar taron Dubar domin ganin yadda kyawawan al’adun mu suke, yadda zasu isa sauran kasashen duniya, a lokacin guda kuma Gwamna Ganduje ya lura da cewa hakan zai kara bunkasa tattalin arziki ta hanyar samar da dama saboda masu sha’awar zuba jari daga kasashen  waje.

 


Advertisement
Click to comment

labarai