Connect with us

LABARAI

Zamba: ’Yan Sanda Sun Cafke Mata Da Miji A Jigawa

Published

on


Rudunar ‘yansanda reshen jihar Jigawa ta ce ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu mata da miji bisa zambatar al’umma ta hanyar katin cirar kudi na ATM yadda suke kwashewa mutane kudade da sunan taimako.Kakakin rundunar ‘yansandan reshen jihar Jigawa SP Abdul Jinjiri ya bayyana haka a yayin da yake baje kolin masu laifin ga manema labarai a jiya a farfajiyar hedkwatar ‘yansanda dake birnin Dutse.

‎Ya ce wadanda ake zargin Rilwanu Sambo Fanti dan shekaru 31 da matarsa Sadiya Rilwanu ‘yar shekaru 29 kuma duk ‘yan jihar Bauchi sun fada komar ‘yansanda bayanda al’ummar birnin Dutse suka kokawa rundunar tasu bisa addabarsu da aka yi wajen zamba a bankuna yayin cirar kudi a katin na ATM.

SP Jinjiri ya kara da cewa, an cafke masu laifin a lokacin da suke yunkurin cire kudi a bankin Eco bank dake Dutse da katin cirar kudin  daya daga cikin wadanda suka basu su taimaka musu wajen cire kudi a ranar 26 ga watan da ya gabata da misalin karfe 11 na rana.

Haka kuma ya karada cewa, kafin cafke su sun damfari wata Hauwa Mustapha kimanin naira dubu 28,000,a yunkurinsu na taimaka mata da katinta na cire kudi.

Sannan kuma sun damfani Sani Garba da Aminu Umar tsabar kudi har kimanin naira dubu 45,000‎ da kuma dubu 50,000 da kuma wani Alhaji Auwalu wadda suka sacewa dubu 435,000 duk a yunkurinsu na taimaka musu su ciri kudi a injin cirar kudin na ATM.

‎Daga karshe ya yi kira ga al’ummar jihar Jigawa da su cigaba da tallafawa yunkurin rundunar ‘yansandan ta hanyar sanar da su duk wani motsi da ba’a gamsu da shi domin daukar matakin da ya da ce.

 


Advertisement
Click to comment

labarai