Connect with us

LABARAI

YEYCON Ta Karrama Shugaban Darikar Katolika Na Bauchi

Published

on


Kungiyar matasan Arewa Maso Gabas wato ‘Northeast Youth Council of Nigeria (NEYCON)’ ta mika lambar yawo wa babban malamin addinin kirista reshen darikar Katolikan da ke Bauchi a bisa rawar da yake tawa na ci gaban zaman lafiya da habaka rayuwar matasa a fadin kasar nan.

Da yake amsar lambar yabon a cambarsa da ke cikin majami’ar St John’s Cathedral da ke Bauchi, Bishop Hilary Nanman Dachelem ya nuna gayar godiyarsa wa kungiyar ta NEYCON a bisa lambar yabon, yana mai kiransu da su yi amfani da samartakansu wajen kyautata zaman lafiya hade da kauce wa tsunduma kungiyoyin ta’adda a kowani lokaci.

Bishop ya ce, “Godiya sosai kan wannan kokarin naku. Ina mai mara wa matasa baya sosai, matukar fa matasan nan suna kwatanta adalci, gaskiya da rikon amana, ko a wace addini ne matashi yake matukar ya rike adalci, gaskiya da rikon amana zai samu sakamako da soyayya a wajen Allah.

“Ina kaunar matasa sosai, ina kallon ci gaban kasar nan ne a kan matasa gaba daya, idan matasa suka ci gaba kasa ta ci gaba, idan matasanmu suka lalace kai tsaye kasa ma ta lalace,” In ji Bishop.

Babban Malamin darikar Katolikan a jihar Bauchi, ya nemi matasan da suke nuna halayen kwarai a kowani lokaci domin ci gaban kasa, daga bisani ya nemi matasan su kaurace wa shiga kowace irin kungiya a shiyyar Arewa Maso Gabas da ka iya kawo tashin hankali da haifar da fitina a tsakanin al’umman yankin domin ci gaban kasar Nijeriya.

Bishop Hilary Nanman Dachelem bai kuma tsaya haka ba, ya nemi matasan su rungumi sana’a da neman ilimi domin gina kasar nan gaba, yana mai nemansu su kaurace wa shiga bangar siyasa da kuma saida mutuncinsu ga ‘yan siyasa masu amfani da su a matsayin ‘yan barandan siyasa.

Ya ce, “Idan matasa suka gudanar da tsaftacaccen siyasa, hakan zai kawo ci gaba matuka gaya ta fuskacin kyautata shugabanci a kasar nan,” In ji Babban Malamin.

Bishop Hilary Nanman Dachelem ya shaida muhimmancin matasa a matsayin hanyar kawo ci gaba wa kasa, don haka ne ya nemi dukkanin masu ruwa da tsaki da su baiwa matasa dukkanin goyon baya domin ci gaban kasar nan.

Tun da fari, shugaban kungiyar Kwamared Aaron ya shaida cewar sun duba cancantar gudunmawar da Bishop Hilary Nanman Dachelem ke bayarwa kan ci gaban zaman lafiya da habaka rayuwar matasa ne suka ga dacewar su karrama shi da wannan lambar ta yabo.

Ya bayyana cewar Bishop ba ma kawai shugaba bane a Nijeriya, ya ce uba ne, kuma alami ne na ci gaban matasa a kowani bigire, don haka suka shaida cewar za su ci gaba da kwaikwayon rayuwarsa a kowani lokaci domin ci gaba da kyautata zaman lafiya da ci gaban kasar Nijeriya

 


Advertisement
Click to comment

labarai