Connect with us

KASUWANCI

Manoman Fulawar ‘Bi Rana’ Za Su Yi Hadin Gwiwa Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Published

on


A makon da ya gabata ne, Kwamishinan ayyukan gona na Jihar Kaduna, ya gayyaci kungiyar manoma fulawar nan da ake kira da, ‘Bi Rana,’ ofishinsa domin su tattauna kan yadda za a bunkasa noman ita wannan fulawar, wacce a turance ake kira da, ‘Sun Flower.’

Duk da shike Kwamishinan bai sami halartar zaman tattaunawar ba, kasantuwar wani aiki na gaggawa wanda ya fitar da shi wajen Jihar, amma dai ya wakilta manyan jami’an ma’aikatar a karkashin jagorancin babban daraktan ma’aikatar, Dauda Ashafa Abubakar, domin su wakilce shi a wajen ganawar.

Bayan fitowarsu daga ganawar ne, wakilinmu UMAR A HUNKUYI, ya zanta da babban shugaban kungiyar na kasa, Jibrin Bukar, domin jin dalilin gayyatar da kuma abin da suka tattauna. A sha karatu lafiya:

Shugaba yanzun muka ga fitowarku daga ofishin Kwamishinan ayyukan gona na nan Jihar Kaduna, masu karatunmu za su so jin dalilin wannan ziyarar naku?

Makasudin wannan ziyarar shi ne, mun zo ne mu gabatar da wannan kungiyar ga gwamnatin Jihar Kaduna, da kuma kara wayarwa da jama’an Jihar Kaduna kai dangane da ita kanta ‘Sun Flower’ din don ba kowa ne ya santa ba.

Mun ji kun gabatarwa da gwamnatin ta Jihar Kaduna da wasu bukatu naku, ko za ka gaya mana bukatun da ku ka gabatar ma gwamnatin?

Bukatar namu dai shi ne, muna son gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya noman ‘Sun Flower’ cikin jerin amfanin gonan da ake nomawa a nan Jihar Kaduna, domin a yanzun, ita ‘Sun Flower’ ba ta daga cikin abin da gwamnatin Jihar Kaduna ta sani na abubuwan da ake nomawa a nan Jihar Kaduna. Na biyu kuma, muna son gwamnatin cikin gonakin da take da su, ta dan tsakurawa wakilan kungiyar namu filin da za su taru a waje guda domin su yi noman ‘Sun Flower’ din, musamman bisa la’akari da yanayin tsaro a halin yanzun. Wannan dai sune manya cikin bukatun da muka nema daga gwamnatin ta Jihar Kaduna.

Ko za ka yi mani karin haske kan ita kanta ‘Sun Flower din nan, domin mutane da yawa ta yiwu sun santa amma ba su san amfanin ta ba?

Da farko dai a hausance ana kiran ita wannan fulawar, ‘Bi rana, ko biya rana,’ dalili kuwa shi ne, ita duk inda rana ta fuskanta, ita ma nan take fuskanta,in rana ta fito gabas ita ma tana kallon gabas din ne, hakanan in tana tsakiya ko yamma, duk tana biye da ranan ne, in kuma ranan ta fadi, sai ka ga ta juya gabas tana jiran ranan ta fito ta sake bin ta.

Tana kuma da fulawowi masu kyau, tana kuma da ‘ya’ya da ganye, ice, sauyoyi da dai abubuwa masu yawa wadanda suke kuma duk masu amfani ne. Daya kuma daga cikin amfaninta shi ne, ana matse mai daga jikin ‘ya’yan nata, man nan kuma sam ba shi da kitse a tare da shi, in ma kuma tana da shi, to kitse ne mai amfani a jiki, ba mai daskarewa ne ba. Man nata kuma mai dadi ne, masu bincike ma suna cewa, daga man Zaitun sai nata a wajen dadi, rashin illa a jiki da kuma amfani. Tana kuma yin magunguna masu yawa, takan zama garkuwa daga cutar ciwon daji, tana maganin sanyin kashi, akalla bincike ya tabbatar da tana maganin cutuka shida ko ma fiye. Sannan kuma ana yin miyan taushe mai dadi mai amfani da ganyenta, ana kuma sarrafa shi kamar yadda ake sarrafa Salad, a kan yi kuma ganyen shayi da shi, wanda kuma duk mai shan shayin ganyen ‘Sun Flower’ zai yi ma shi maganin gudawa, zai masa maganin zazzabi sannan kuma zai ma shi maganin ciwon zuciya. Bayan kuma mai da ake cirewa daga jikin ‘ya’yan, a kan kuma yi abincin dabbobi da kaji da dusar, a kan kuma sarrafa ‘ya’yan a yi man shafawa, sabulun wanka da na wanki duk da su. Saiwarta kuma ana yin maganin cizon maciji da ita, da kuma cutar Tautau, wannan kadan ne daga cikin amfanin wannan dan tsiro mai albarka a gurguje.

A nan kasar ne aka gano amfanin wannan tsiron na ‘Sun Flower,’ ko kuwa wasu kasashen na duniya ma suna amfani da shi?

Ai kasashen duniya da yawa sun yi gaba a sanin amfaninta da kuma cin moriyar amfanin nata, bilhasali ma, duk wani babban mutum da za ka tambaya, in dai zai gaya maka tsakani da Allah, ba sa cin duk nau’ukan man gyadan nan da muke ci, daga man ‘Sun Flower’ sai kuwa dai man zaitun ne kadai suke ci, da ire-iren su. Saboda a yanzun sai dai a shigo mana da man masu hali daga cikinmu suna sayansa da dan karen tsada, wani bincike ma da muka yi, mun gano cewa, gwamnatin tarayya ta yi asarar sama da Naira bilyan 1.6 wajen shigo da man ‘Sun Flower’ a kasarnan, wanda da muna sarrafa ta da duk ba mu yi wannan asarar ba.

To yanzun a nan Jihar Kaduna ne ku ka fara kokarin aiwatar da wannan shirin ko kuwa akwai wasu Jihohin?

A’a, ina fa! Ai Jihar Kaduna za dai mu iya cewa, yanzun ne take son shiga cikin shirin tsundum, amma ai Jihohin kasarnan da yawa tuni sun yi nisa. Misali kamar Jihohin, Gombe, Kano, Bauci, da sauransu. Jihar Bauci ma a yanzun haka, sun baiwa wannan kungiyar tamu makeken filin da za ta yi noma, sun ba mu motar tarakta, sun ma bamu ofishi na musamman, da dai abubuwa masu yawa. Sannan kuma babban ofishinmu yana Abuja ne, gwamnatin tarayya tana taimaka mana sosai, hatta injunan sarrafawa da tace man nata duk gwamnatin tarayya ta yi mana alkawarinsu. Hakanan a Jihohin kudanci da yammacin kasarnan, duk muna da jama’a a wuraren, misali Jihohin, Oyo, Bayelsa da sauransu, duk akwai manoma ‘Sun Flower’ a wuraren.

Wannan ya nu na a kan iya shuka ‘Sun Flower’ a ko’ina kenan?

A kan shuka ta a duk inda ba ya tara ruwa, ita babban abin da ba ta so shi ne ruwa ya kwanta a karkashinta, indai za a yi ruwa yanzun ya kuma wuce, to ita wannan ba damuwarta ba ne.

To wane irin tarba ne Kwamishinan ayyukan gonan ya yi maku kan wannan shawarwarin da ku ka zo ma gwamnatin da shi?

Gaskiya Kwamishina da mukarrabansa sun karbe mu hannu bibiyu, sun kuma yi murna da mu da kuma shawararwarin da muka zo masu da su sosai. Kuma ma nan take har sun amsa mana wasu daga cikin bukatun da muka nema a gare su, wasun kuma suka ce mu je mu zo masu da su a rubuce, duk sun yi alkawarin za su yi mana.

Akwai wani kiran da kake da shi ga al’umma dangane da wannan noman na ‘Sun Flower’?

Kira na ga al’umma shi ne, don Allah mu yi kokari mu nomi wannan tsiron na ‘Sun Flower’ ko da ba domin man nata ba, ai a kan yi magunguna da shi, sannan kuma man nata ya ma fi na mangyada amfani da rashin illa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai