Connect with us

LABARAI

Kawar Da Cutar Shan Inna: An Yaba Wa Shugabannin Kananann Hukumomin Kano

Published

on


Kamar yadda gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ke bakin kokarinsa wajen kawar da cutar Poliyo a tsakanin kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar, an tabbatar da suma shugabannin kananan hukumomin jihar sun bi sahun gwamnan na Kano domin kawar da cutar daga jihar baki daya daga kananan hukumominsu.

Da take zantawa da manema labarai a rana ta biyu na fara gudanar da rigakafin cutar a karamar hukumar Nassarawa dake jihar ta Kano, babbar jami’ar kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar Hajita Saratu Ibrahim, ta ce daga lokacin da aka ara digawa kananan yara maganin na Poliyo, an samu nasarorin da ake bukata domin duk inda aka je ba a samun matsala daga iyayen yara.

Hajiya Saratu Ibrahim ta kara da cewa, ko kafin gudanar da shirin karo na uku cikin wannan shekarar a shekarun baya ma shirin na samun nasarori sosai tun daga kan iyaye har ya zuwa yaran da ake digawa rigakafin cutar.

Shugaban karamar hukumar Nassarawa, Hon. Lamin Sani na matukar taka rawa da goyon baya wajen ganin an samun nasarar aiwatar da shirin tare da kawar da cutar daga karamar hukumar ta Nassarawa duk da kasancewar babu wani yaro ko daya da yake dauke da cutar a yankin inji Malama Saratu Ibrahim.

Duk abin da ake bukata Lamin Sani yana bayarwa musamman yadda ya sayi manya manyan Firinji guda biyu dake sanyaya magungunan cutar tare da sayan janareto guda daya ta yadda da zaran babu wuta sao a tayar da janareto.

Domin ganin harkokin lafiya sun inganta yanzu haka ya dauki ma’ikatan lafiya na wucin gadi 381 da ake biyansu albashi duk wata, tayi amfani da wannan dama da jinjina wa gwamnan jihar game da kokarin da yake aiwatarwa na kakkabe cutar daga hjiar baki daya a jihar dama sauran cututtuka.

Daga karshe Saratu Ibrahim ta ce, tana fatan sauran gwamnatoci za su ci gaba da bai wa harkokin lafiya muhimmanc kamar yadda gwamnan jihar Kano keyi.

Ita ma da take na ta jawabin ga manema labarai game da aiwatar da shirin na rigakafin cutar ta Poliyo a karamar hukumar Dala, jami’ar kula da lafiya amatakin farko na karamar hukumar Hajiya A’isha Sani Wali, ta ce hakika ta samu nasara sosai a lokacin gudanar da shirin na poliyo, musamman yadda ta samu hadin kai da goyon baya daga iyayen yara.

Sai tayi amfani da wannan dama da godewa shugaban karamar hukumar ta Dala, Kwamared Ibrahim Ali Yantandu, a kan hadin kan da yake bayarwa domin ganin an samu nasara kawar da cutar a yankin baki daya.

Shi ma hakimi dakatai da masu unguwannin kan taimaka a duk lokacin da za a gudanar da poliyo, bayan kula tare da sanaya ido da shugaban karamar hukumar keyi a kan yakar cutar poliyo haka kuma yana kula da sauaran harkokin lafiya a yankin wannan ya sa inji A’isha karamar hukumar ke kan gaba wajen kula da lafiyan al’umma a cikin kana nan hukumomin jihar 44.


Advertisement
Click to comment

labarai