Connect with us

LABARAI

Fayose Ya Zargi ’Yan Sanda INEC Da Fayemi A Bisa Yunkurin Murda Zabe

Published

on


Gwamnan jihar Ekiti mai shirin barin gado, Ayodele Fayose, ya zargi ‘yan sanda da sashen jami an farin kaya na na DSS, don sake maida wa da tsohon gwamanan jihar Kayode Fayemi da manyan jami’an tsaronsa don kulla tuggun tabka magudin zaben gwamnan da za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli.

Babban jami’in tsaron, Hakeem Abiola da kuma tsohon jami’in tsaron mai suna Adeyemi Ajayi, za su sanya ido ne kan manyan gwamnatin da wasu jami’an tsaro na jihar da ake zargin sun yi sama da fadi da dukiyar jihar.

A sanarwar da gwamnan ya yi ta kafar yada labaran jihar a garin Ado Ekiti ranar Litinin din da ta gabata, ya kara jaddada zarginsa akan cewar, Shugabar hukumar zabe ta kasa uwargida Aminat Zakari, da kuma wasu jami’an hukumar uku suna yi wa Fayemi aiki ne, Hakeem tuni yana garin Ado Ekiti ya bude otel a titin Iworoko.

Sai dai Zakari a jawabinsa a wurin wani taron bita da aka gudanar a Ado Ekiti ya yi watsi da zarge-zargen Fayose, inda ya ce zai yi wuya a yi murdiya a lokacin zaben, kuma Fayose ya futar da hujja akan zargin nasa bayan jami’an tsaro sama da 20,000 ne za su sanya ido akan zaben domin mu a INEC babu wani abu da muke boyewa, nufin mu kuma shi ne a gudanar da zabe mai tsafta da kowa zai yi na’am da shi. Sunayen jami’an hukumar da gwamnan yake zargi tare da kwamishiniyar zabensu ne, Mista Kenneth Ukeagu, da Paschal Uwaenwe, da kuma Abdulrazak Yusuf.

Gwamnan ya yi zargin cewar, Uwaenwe da Agboola za su tura na’urar zabe marar kyau da latatattun kayan zabe zuwa Ado Ekiti da Ikere, inda kuma Kenneth Ukeagu zai samar da takardun jefa kuri’a da aka dangwale su, aka kuma saka a cikin akwatin zabe dake dauke da fam mai lamba EC8 A, EC8 B, da kuma EC8 C, har da wasu manyan kayan zabe, har ila yau, fam masu dauke da lamba iri daya, inda za a mika wa Fayemi don canza sakamankon zaben mazaba mai lamba 503.

Fayose ya kara da cewar, ana shirin chanza masu yi wa kasa hidima da sunayen dalibai na jamiar tarayya ta oye Ekiti dana kwalegin kimiyya da fasaha dake a matsayin jami’an zabe da za a tura Ado Ekiti, da kuma sanya wasu ‘ya’yan APC. Har ila yau, Mrista Akin Fakorede na sashen jami’an ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi na tarayya, za a tura shi zuwa jihar a matsayin na riko don gudanar da zaben, inda ya ce, har yanzu ‘yan Nijeriya ba su manta da rawar da Akin Fakorede ya taka a zaben jihar Ribas ba, kuma irin hakan ne suke son su mai-maita a Ekiti.

Ya kara da cewar, jami’an ‘yan sandan da aka wadata su da makamai, jami’in tsaron Fayemi ne zai lura da su shi da Akin Fakorede, kuma dukkansu za su yi wa mazabar mai lamba 503 kawanya don yin harbin kan mai uwa-da-wabi su saci kuriu. Ya kuma yi tambaya akan cewar, me ya sanya ‘yan sanda da DSS suka turo tsohon jami’i mai kare lafiyar Fayemi zuwa jihar don sanya ido akan zaben?

Ya yi kira ga shugaban ‘yan sanda Ibrahim Idris, da Daraktan DSS Lawal Daura, da su bari a gudanar da zabe mai tsafta a, haka kuma Shugaban hukumar zabe ta kasa Mahmood Yakubu, ya ja kunnen ma’aiktan hukumar akan yunkurin barin a yi amfani da su don a murda zaben.

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan kasashen waje da su sanya ido sosai akan INEC, musamman sunayen wadanda ya bayyana yana zargin za a yi amfani da su don a murda zaben. Kakakin yakin neman zaben Kayode Fayemi, Wole Olujobi, ya karya ta zarge-zargen gwamnan inda ya ce tuni gwamnan ya yi kaurin suna da yin zagi akan mutane ba tare da wata kwakkwarar hujja ba. Haka shima shugaban yan sanda, Ibrahim Idris, yace yan sanda baza su sanya jan su a cukin siyasar jahar kyma zasu gudanar da aikin su kamar yadda doka ta tanafa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai