Connect with us

LABARAI

Zargin Badakalar Dala Milyan 40: Dan’uwan Jonathan Ya Kasa Kare Kansa Daga EFCC

Published

on


Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Jihar Legas, ta yi watsi da tuhumar keta haddi wacce Robert Azibaola, wanda dan’uwa ne ga tsohon shugaban kasarnan, Goodluck Jonathan, ya kai gabanta, inda yake tuhumar hukumar EFCC da keta masa haddi.

Alkalin kotun, Ojisola Olatroegun, cewa ya yi, wannan karar da Mista Azibaola, ya kai a gabanta keta alfarman kotu ne, domin kuwa ya kai kwatankwacinta a wasu kotunan.

Alkalin ya ce, hukumar ta EFCC, ta yi aiki ne daidai da hurumin da doka ta tanadar mata kan bincikar da take yi wa Mista Azibaola din.

Mista Azibaola, ya kai karar hukumar ce ta EFCC a kotun inda yake tuhumarta kan kamu da tsare shi din da hukumar ta yi bisa zargin sa da handame dala milyan 40.

Cikin wadanda ya shigar a cikin karar har da, babban mai shari’a na kasa, da kuma gwamnatin tarayyan kanta.

Cikin takardar karar da ya shigar, wacce, Faith Robert, wani malami a Jami’ar Neja Delta, ta Jihar Bayelsa ya yi rantsuwa a kanta, Mista Azibaola, ya kwatanta kusancin da yake da Mista Jonathan, a matsayin dalilin da ya sanya wasu makiyan tsohon shugaban kasar suke ta azabtar da shi, domin neman wai tilas sai ya tsunduma Jonathan din a cikin aikata laifi ko ta halin kaka.

A cikin rantsuwar ta Mista Azibaola, cewa ya yi, a wani lokaci ne na shekarar 2012, marigayi Patrick Azazi, wanda tsohon Janar din Soja ne, kuma tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ya neme shi a bisa sanin da ya yi masa na iya dakatar da matsalolin satan mai da kuma lalata bututun man.

A kan hakan ne a watan Satumba na shekarar 2014 aka biya dala milyan 40 a asusun ajiyar kamfanin, Oneplus Holdings Nigeria limited, domin gudanar da aikin, bisa yarjejeniyar za a biya shi kashi 10 na wannan kudin.

Sai dai kuma, bayan da aka sami canjin gwamnati ne a watan Mayu na shekarar 2015, sai aka kafa wani kwamiti domin ya sake duba yadda gwamnatin baya ta bayar da wasu ayyuka, a nan ne aka bukaci wannan kamfani na, Oneplus Holdings Nigeria limited, da ya maido da kudin dala milyan 40 nan take.

A nan ne, Mista Azibaola ya ce, an tsare shi a bisa umurnin wata kotun majistare bisa tuhumarsa da barnata dukiyar gwamnati.

A nan ne ya bukaci kotun da ta bayyana kamu da tsare shin da aka yi da cewa take masa hakki ne.

Ya kuma sake neman kotun da ta hana wadanda yake karan sake ci masa mutunci da keta masa ‘yanci ta hanyar sake kama shi da kuma tsare shi.

A takardan martanin da Lauyan hukumar ta EFCC, Idris Mohammed, ya yi rantsuwa a kanta, cewa ya yi, a wani lokaci ne na watan Nuwamba na shekarar 2015, hukumar ta sami wani bayanin sirri kan Mista Azibaola, kamfaninsa da kuma wasu, kan wata kwangilar bogi da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, ya ba shi.

Hukumar ta EFCC ta ce, ta gano a tsakanin shekarar 2012 zuwa watan Maris na shekarar 2015, Sambo Dasuki, ya bayar da ayyukan kwangilolin bogi masu yawa, ga kamfanoni daban-daban, wanda kudinsu ya kai Naira, 2,219,188,609; Dala,1,671742,613; da kuma Yuro, 9,905,477.

Hukumar ta EFCC ta ce, Sambo Dasuki, ya umurci babban bankin kasarnan da ya biya Naira milyan 650 ga kamfanin, Tunji Adeniyi & Co, domin ya sayi wasu kadarori a fuloti mai lamba,  2245 da ke Maitama Cadastral, domin amfanin Mista Azibaola, da kuma wasu dala milyan 40 ga kamfanin, Oneplus Holdings Limited domin ya sayo wasu makaman yaki.

Duk kuma an bayar da kudaden ba tare da bayar da wani aikin kwangila ba.

Hukumar ta EFCC ta ce, Mista Azibaola, ya karbi kudin dala mliyan 40 ya kuma zuba su cikin aljihunsa domin gararin kansa da kuma wasu. Ya yi zargin wai ya yi amfani ne da kudin wajen aiwatar da wasu ayyukan kwangila da wasu kamfanoni tare da taimakon matarsa, Stella Robert, da kuma jami’insa na kudi, wani mai suna, Amobi Agun.

Hukumar ta EFCC ta ce, a kokarin da ya yi na boye badakalar na shi ne, kamfanin na, Oneplus Holdings ta hanyar Mista Azibaola da matarsa, suka yi umurni da a mayar da dala milyan 1.5 ga kamfanin ReyaTelecommunications Limited, wanda shi kuma daga bisani ya biya dala milyan 1.4 ga kamfanin NETSPACE Telecommunications.

Hukumar ta EFCC ta ce, a lokacin da take bincikar kamfanin na, Oneplus Holdings a watan Mais 24, 2016, ta gano takardun da ke nu ni da cewa, wata mai suna, Robert da wani mai suna, Dike Ndubuisi sun karbi dala,7,556,000 tsaba a tsakanin ranar 17, ga watan Oktoba 2014, da kuma ranar 27 ga watan Janairu, 2015, wanda suka canza su zuwa Naira, 1,344,208,000 domin amfanin kashin kansu

Hukumar ta ci gaba da cewa, Mista Azibaola da matarsa, tare da taimakon jami’insu na kudi, sun sake tura dala milyan biyu zuwa ga wani kamfani mai suna, Capital Field Inbestment, da wata dala milyan biyun ga asusun wani mai suna, Kamaludeen Dahiru.

A wani binciken kuma da hukumar ta yi, ta gano cewa, Mista Azibaola, a lokacin da yake mukaddashin babban darakta a kamfanin, Mangrobetech Construction and Engineering Company Nigeria Limited, wanda yanzun ya zama, Kakatar Ce Limited, ya karbi Naira bilyan 2,504,917,058 daga hukumar kula da ruwayen Nijeriya,  ‘Nigerian Maritime Administration and Safety Agency,’  ya kuma yi shagalin gabansa da su.

Hukumar ta EFCC ta ce, bayan kiyawar da ya yi ne na ya karba kiran da ta yi ma shi na ya kawo kansa ofishin hukumar, sai Mista Azibaola, ya fito ya nu na kansa domin ya gujewa shelanta nemansa, daga nan kuma ya shiga ‘yar buya a tsakaninsa da jami’an hukumar ta EFCC, wanda hakan ne ya tilasta wa hukumar da ta nemi izinin kama shi daga wata kotun ta Abuja.


Advertisement
Click to comment

labarai