Connect with us

LABARAI

Matakan Da Oshiomhole Zai Bi Ya Ci Nasara -Sanata Marafa

Published

on


Shugaban kwamitin Majalisar Dattijai a kan harkar man fetur, Sanata Kabiru Garba Marafa, sanata mai wakiltar jam’iyyar APC daga jihar Zamfara ya zayyana matakai guda biyar da sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa Kwamrade Adams Oshiomhole zai dauka in har yana bukatar samun cikakken nasarar jagorancin jam’iyyar.

Bangare jami’yyar APC da Sanata Marafa ke jagoranta a jihar Zamfara ta shirya tarukkan jamiyyar tare da zaban shugabannin jam’iyyar haka kuma sun zabi wakilai zuwa babban taron jam’iyyar da aka yi a Abuja amma ba abar wakilansu suka shiga filin taron ba, wakilai daga bangaren Gwamnan Abdulaziz ne aka amince dasu a wajen taron.

A tattaunawar da ya yi da wakilinmu ta kafar WhatsApp, Sanata Marafa ya bayyana aniyarsa na takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara, ya kuma bukaci shugaban jamiyyar Adams Oshiomhole ya gudanar da jahorancin jam’iyyar tare da bin dokokin tsarin mulkin jamiyyar.

Ya shawarci Oshiomhole da kada ya yi katsalanda a harkokin tafiyar da jam’iyya a matakan jihohi sai dai inda aka samu matsaloli masu yawa.

“Ya kamata a ba wasu shugabannin jam’iyyar tikitin takara kai tsaye don a samu a rage rikice rikicen da kuma kurar da babban taron jamiyyar ya tayar,” inji shi.

Ya shawarci Oshiomhole da cewar, “Ya gaggauta yin nadzari da kuma lura da karfin mambobin kwamitin zartasawarsa da nufin gano wadannda suke da akida iri daya da kuma wadanda zai iya aiki tare dasu ta haka ne zai taimaka masa wajen tantance baragurbi da munafukai da zasu iya kawo masa cikas da nasarar da ake bukata a zabukan dake tafe na shekarar 2019.

Sanata Marafa ya kuma ce, “Dole Oshiomhole ya yi tsayin daka wajen fuskantar baragurbin ‘yan siyasa da aka dasa a cikin tafiyarsa donmin biyan bukatar iyayen gidansu, ta hanyar karkatar da alkiblar jam’iyyar zuwa yadda iyayen gidansu ke bukata, ya kamata kuma ya yi hakan ne ba tare da tsoro ko jin kunyar wani ko wata ba, kamar dai yadda muka gani a babban taron jam’iyyarmu da aka gudanar kwanakin baya.

“Ya kamata ya kuma fahinci cewar, duk wani dan siyasar dake jin tsoron fuskantar zabe to bashi sa zuciyar da ya kamata ya shiga harkokin siyasa. Ya yi kokarin yin maganin ‘yan baranda masu dagula lissafi daga kasa hae sama don kuwa irin wadanna mutanen makiya harkar siyasa ne, ya kuma kamata ya yi kokarin yin mulki cikin adalci tare da kawo sulhu tsakanin ‘yan jam’iyya daga dukan bangarorin kasar nan, kada yab yarda a yi amfani da shi wajen kawo rarraba a tsakanin ‘yan jam’iyya.” Inji shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai