Connect with us

LABARAI

Kungiyar Matasa Ta Yabawa Shekaru Uku Na Wakilcin Sanata Wamakko

Published

on


Kungiyar Matasan Sakkwato ta Arewa masu fafutukar ci-gaban Jihar Sakkwato ta bayyana cewar shekaru uku na wakilcin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a Majalisar Dattawa ya taka muhimmiyar rawa wajen sauke nauyin da al’ummar mazabarsa suka dora masa.

Kungiyar a karkashin jagorancin Honarabul Naseer Bazza ta bayyana cewar Wamakko wanda ke wakiltar Sakkwato ta Arewa a Majalisar Dattawa ta Takwas daga 2015 zuwa yau ya samu nasarar gabatar da Dokoki da Kudurori domin ci-gaban al’ummarsa da al’ummar kasa bakidaya haka ma ya gudanar da muhimman ayyukan raya mazaba da ci-gaban al’umma.

Ya ce don haka “Ko kadan babu kanshin gaskiya kan bayanan da kungiyar Sakkwato Birnin Shehu ta fitar a kafar sadarwa ta yanar gizo cewar Tsohon Gwamnan na Sakkwato bai aiwatar da ayyukan raya mazaba ba wadanda ke a cikin Kasafin Kudi na 2017 ba. Ina son jama’a su sani wannan maganar ba ta da tushe ballantana makama kuma kungiyar da ta yi wannan bayanin kungiya ce marasa alkiblar siyasa wadda ke tare da mutane masu hassada da kyashi da kiyayya ga siyasar Sanatan da ba ya da shinge.” In Ji Bazza.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewar Sanata Wamakko wanda shine Shugaban Kwamitin Ilimin Furamare da Sakandire a Majalisar Dattawa bai karbi kudin gudanar da ayyukan yanki ba akasin yadda kungiyar ke tunani tare da cewar tuni har Hukumar Yaki da Almundahana ta EFCC ta gayyaci Sanatan kan wannan batun mai kama da almara.

A cewarsa “Ya na da kyau a fahimci sanya aiki a cikin Kasafin Kudi da bayar da dama don gabatar da aikin da kuma fitar da kudi don a yi aikin dukkansu suna da bambanci. A lokuta da dama Gwamnatin Tarayya za ta sanya aiki a Kasafin Kudi ta kuma bayar da dama don gudanar da aikin, amma kuma ta kasa fitar da kudi don yin aikin. Wannan shine babban misalin da yake faruwa a mafi yawancin ayukkan ‘yan Majalisar Tarayya ba wai kawai ga Sanata Wamakko kadai ba.” In ji kungiyar.

Hon. Bazza ya bayyana cewar masu irin wannan tunanin makafi ne wadanda idanunsu suka rufe ga ganin ayyukan wakilci da Sanata Wamakko ke yi da kudin aljihunsa ba wai a iya mazabarsa kawai ba, a fadin Jiha bakidaya wanda a kan hakan ne ya samu inkiyar Sanatan da ba ya da shinge wanda ya ce a zamanin Gwamnatinsa ta shekaru takwas ya gudanar da shugabanci nagari abin koyi da kwatance.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewar ko kadan ba wai ya yi magana ba ne domin mayar da martani ba sai dai domin fayyace gaskiyar lamari a wakilcin Sanata Wamakko wanda ya aiwatar da muhimman ayyuka a fannin ilimi, kiyon lafiya, aikin goma, samar da ruwan sha, karfafawa mata da matasa, samar da ayyukan yi da taimakawa al’umma.

“Wamakko ya dauki sha’anin ilimi da matukar muhimmanci, ya bayar da tallafin karatu ga daruruwan dalibai a ciki da wajen kasar nan wadanda ke karatu a Ingila, Pakistan, Saudiyya, Ghana, Benin, Sudan da Jamhuriyar Nijar a digiri na daya, na biyu da na uku wadanda ba ya ga daukar nauyin karatunsu ya kan kuma ziyarce su a makarantun su domin karfafa masu guiwar dagewa da karatu. Kwanan nan ma Sanatan ya dauki nauyin karatun dalibai 80 ‘yan Karamar Hukumar Gudu domin samun takardar Malanta ta NCE.” Ya bayyana.

Ya ce “Sanata Wamakko ya baiwa manoma takin zamani da irin noma daban-daban da samar da rijiyoyin noman rani da na zamani tare da injunan ban ruwa da magunan kashe kwari a dukkanin Kananan Hukumomi takwas da yake wakilta domin bunkasa sha’anin noma da kiyo a mazabarsa wadda ke da kasar noma mai kyau.”

Ya ce “Aikin daukar nauyin duba lafiyar idanun kyauta da Wamakko ya yi a mazabarsa ya haifar da da mai idanu domin mutane 1, 830 ne suka amfana da aikin irinsa na farko a mazabar. Haka ma an fadada aikin a sauran Kananan Hukumomi 19 a inda mutane 3, 000 suka ci gajiyar shirin.” Ya bayyana.

Hon. Naseer Bazza ya bayyana cewar a yanzu haka Wamakko ya gina Cibiyar Fasahar Sadarwar Zamani (ICT) wadda ke daukar mutane 500 a lokaci daya wadda aka samar domin samun ingantaccen ilimin fasahar sadarwa tare da horas da malaman makarantu domin samun kwarewar gudanar da aiki yadda ya kamata. Ya ce haka kuma za a rika gudanar da jarabar shiga jami’a ta JAMB a cibiyar wadda itace irinta ta farko a Sakkwato.

 


Advertisement
Click to comment

labarai