Connect with us

LABARAI

Buhari Na Kaunar Nijeriya Fiye Da Kansa –Ganduje

Published

on


Gwamna jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari cikakken dan kishin kasa ne wanda yake tsananin son nijeriya fiye da yadda yake son kansa.

Ya ce, shugaba Buhari jagora ne mai kishin kasa kuma mutum ne mai mutunci da gaskiya da rikon amana.

Gwamna ganduje ya yi wadannan kalaman ne ranar litinin a taron cin abincen dare da jam’iyyar APC na sashin kudu maso gabas ta shirya don karrama shugaba buhari a garin Owerri, babban birni jihar Imo, taron ya gudanat ne a gaban sabbin zabbabun shugabannin jam’iyyar APC na yankin.

Sanarwar da aka rabawa ‘yan jarida wadda jami’in watsa labaran gwamna Ganduje, Abba Anwar, ya sanya wa hannun ranar Talata tayi bayanin yadda taron ya gudana.

“Buhari alama ne na hadin kan kasa, Buhari yana matukar son Nijeriya fiye da yadda yake son kansa, yana kuma hankoron ganin ya kawo ci gaba ga kasarmu a dukkan lokaci, wannan taron karrama shi ya yi dai dai,” inji Gwamnan.

“Kafin hawan shugaba Buhari karagar mulki ana samun tashe tashen bama bamai a yankin Arewa maso gabas gaba daya wurare irinsu kano ma basu tsira ba, mun shiga matsala kwarai da gaske.”

Ya kara da cewa,“A kwai lokacin da aka kai hari ofishin ‘yan sanda guda 10 a lokaci daya inda fiye da mutum 30 suka mutu. Muna kara tuna lokacin da aka tayar da bama bamai a babban masallacin jumma’a na kano inda a nan kuma aka kashe mutum fiye da 200, dukkan wadannan hare haren ‘yan kungiyar Boko haram suke kai wa. Amma a halin yanzu dukka wadanna sun zama tarihi tun lokacin da shugaba Muhammadu buhari ya zama shugaban kasa.”

Gwamna Ganduje ya kuma kara da cewa, kafin jam’iyyar APC ta karbi jagorancin kasar nan sojoji na fuskantar matsala wajen tafiyarbda aikinsu, basu da makaman kirki basu kuma da kwarin gwiwar fakin da suke yi da ‘yan ta’adda a lokacin.

“Amma a lokacin da shugaba Buhari yah au karagar mulki abubuwa sun gyaru komai ya fara aiki yadda ya kamata, gaba daya Buhari na Nijeriya ne, in muna neman mutumci to Buhari ne mansarmu. In muna neman gaskiyar da za a ia yakar cin hanci da rashawa, Buhari ne amsa,” inji shi.

A kan babban taron jam’iyyar APC na kasa da aka gudanar, Mista Ganduje ya yi watsi da dukkan has ashen da ake yin a cewar, jam’iyyar zata tarwatse bayan babban taron jam’iyyar. “Ina masu fatan cewa, jam’iyyar zata wargaje bayan an kammala babban taron jam’iyyar, jajircewar Shugaba Buhar ya sa aka gudanar da taro cikin nasara, za kuma mu ci gaba da samun nasara a nan gaba,” inji shi.

“Babban taron nasara ce ga daukacin Nijeriya, nasara ce ga yankin Kudu maso Gabas nasara ce kuma ga siyasar jihar Imo baki daya.”

Gwamna Ganduje ya kuma yi magana a kan zargin cewa, an so a wulakanta gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo a wajen babban taron jam’iyyar APC da aka yi.

Ya kuma bayyana matakan daya dauka a lokacin da wasu matasan yankin Arewa suka ba ‘ya kabilar Ibo dake zaune a jihohin Arewa 19 wa’adin barin yankin Arewa, gwanduje ya yi bayanin yadda ya nemi izimin shugaban kasa wajen kawo karshen tashin hankalin da aka fuskanta a lokacin.

“Na je wajen shugaban kasa na nemi ya bani izinin sasanta lamarin, nan take shugaba Buhari ya ce in ci gaba. Na kira taron kungiyarb matasan arewa tare da shugabannin kabilar Ibo dake a fadin yankin jihohin arewa 19 inda muka yi taron na tsawon kwanaki 5 a garin kano,” inji shi. “Taron ya yi armashi kwarai da gaske, bayan taron ne matasan suka tafi Abuja inda suka janye wa’adin da suka bayar, mun yi imanin bin lalama wajen magance dukka wani matsala.”

A wajen taron ne aka gabatar wa Gwamna Gwanduje sabbin shugabannin jam’iyyar APC na yankin da kima shugabannin jam’iyyar na jihohin yankin gaba daya.

An yi matukar jijina wa da nuna godiya ga jawaban da Gwamna Ganduje ya yi a wajen taron.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Imo Mista Okorocha ya yaba wa jihar Kano, musamman a kasanewarta na jihar da tafi karbar ‘yan kabilar Ibo fiye da ko ina a fadin kasar nan.

Wannan ya na nuna irin halin karamci ne irin na Kanawa, a iya sani na gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ‘Mai Gandujiyya’ mutum ne tsayayye mai neman hadin kan ‘yan Nijeriya,”inji Mista Okorocha.


Advertisement
Click to comment

labarai