Connect with us

LABARAI

’Yan Boko Haram Sun Yi Wa Na’ibin Liman Yankan Rago A Borno

Published

on


A ranar Asabar da dadare ne wasu ‘yan kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi wa wani na’ibin limamin masallacin jumma’a tare da wasu mutum biyu a garin Gajiram, dake karamar hukumar Nganzai ta jihar Barno.
Bayani ya nuna cewar, ‘yan ta’addan sun mamaye gidan limamin ne mai suna Imam Mallam Babagana da na’ibinsa Mallam Mukhtar tare da wasu mutum biyu iunda suka yi musu yankan rago.
Wani mazaunin garin Goni Gajiram, ya ce, ‘yan ta’addan sun kuma sace garken shanu a harin da suka kawo da tsakar dare. Har yanzu rundunar sojoji dake aiki a yankin basu ce komai ba aka al’amarin.
Mazauna yankin sun ce kusan kullum sai ‘yan ta’adda sun mamaye tare da kai hari garurwar dake kewayen yankin.
“A kullum sai ‘yan Boko Haram sun kai hari kauyukan dake yankin, a makon jiya ne ma ‘yan Boko Haram suka kawo hari a cikin manyan motoci har 11 inda suka kashe mutum 9.
“Kauyuka kamar Birimari da Goni da Abachari da kuma Monguno na fuskantar harin ‘yan book haram a kusan kullum, muna shirin kai kukanmu ga gwamna don ya kawo mana ceto.” Inji Mista Gajiram.


Advertisement
Click to comment

labarai