Connect with us

LABARAI

NNPC Ta Bada Tallafin Miliyan 50 Ga Wadanda Guguwa Da Gobara Ta Shafa A Bauchi

Published

on


Hukumar Albarkatun Danyen Man Fetur ta kasa (NNPC) ta bayar da tallafin naira miliyan hamsin ga wadanda ibtila’in mamakon ruwan sama da wadanda gobara ta yi musu barna a jihar Bauchi kwanakin baya.
Shugaban hukumar ta NNPC, Dakta Maikanti Baru Kachalla shine ya shelanta bayar da tallafin a jiya Lahadi, sa’ilin da ya jagoranci ma’aikatan NNPC kai ziyara ga Sarkin Bauchi domin jajantawa hade da nuna alhenin kan ibtila’I guda biyun da suka auku a jihar Bauchi.
Ziyarar wadda ta gudana a fadar mai martaba Sarkin na Bauchi, da yake bayani kan tallafin da suka kawo jihar, Baru ya shaida wa sarkin cewar wannan tallafin na zuwa ne daga cikin asusun hukumar na tallafa wa jama’a, don haka ne suka yanke shawarar kawo daukin zuwa ga wadanda lamarin ya shafa domin rage musu radadi.
Dakta Maikanti Baru ya misalta ibtila’in daga Allah, inda ya nuna gayar damuwarsa kan adadin wadanda lamarin ya shafa, don haka ne nemi su rungumi hakan daga Allah, hade da komawa gareshi don samun sauki.
Daga bisani Babban Daraktan gudanarwa na kamfanin mai din, ya kuma yi amfani da damar wajen mika sakon ta’aziyyar rasuwar Katukan Bauchi da Alhaji Ahmadu Yari.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Darakta a sashin kula da aiyukan kamfanoni da tsare-tsare na hukumar ta NNPC, Alhaji Bala Wunti ya bayyana cewar hukumarsu ta damu gaya kan ibtila’in da suka auku a Bauchi, don haka ne ma suka kawo wannan tallafin zuwa jihar domin rage wa jama’a radadi.
Da yake maida jawabinsa, mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji (Dakta) Rilwanu Suleimanu Adamu ya jinjina wa hukumar albarkatun man a bisa wannan gagarumin gudunmawa da suka kawo jihar, yana mai addu’ar Allah ya saka musu da alkairinsa.
Wakilinmu ya labarto kan cewar NNPC bayan gabatar da sakon jajenta a baki, sun kuma gabatar da jajensu ga jama’an jihar Bauchi a rubuce wanda suka mika wa Sarkin Bauchi.


Advertisement
Click to comment

labarai