Connect with us

LABARAI

Mace Ta Hada Baki Da ’Yarta Wurin Kashe Mijinta

Published

on


A ranar Litinin ne wata babbar kotun Abuja ta bayar da umurnin garkame a gidan yarin Suleja, wata matashiya da ta hada baki da da uwarta wajen kashe ubanta a kauyen Kusha Kure.
Mai shari’a Idris Kutigi, ya bayar da umurnin ci gaba kulle wadanda ake zargin ne bayan da suka amsa laifin da ake yi musu na hada baki tare da kisan kai.
Mai Shari’a Kutigi, ya dage karar zuwa ranar 19 ga watan Satumba do ci gaba da sauraron karar.
Dan sanda mai gabatar da kara, Mista Fidelis Ogbobe, ya bayyana wa kotun cewa, an aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Maris.
Ya ce. Matashiyar da mahaifiyarta, dukkansu masu sana’ar sayar da itace ne a kauyen Karaban dake karamar hukumar Bwari a yankin Abuja, sun Sassari Kure ne da dada har ya mutu a gidansu dake Karaban a ranar 10 ga watan Maris.
Ya kara da cewa, matashiyar ta aikata wannan danyan aikin ne saboda marigayyin ya kasa daukar nauyinta da saurayinta dan shekara 24. Laifin ya saba wa sashin dokan Penal code na 97 da 221, hukuncin laifin kuma yana a sashi na 221 duk dai a dokar Penal Code.


Advertisement
Click to comment

labarai