Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Sake Bayar Da Belin Sambo Dasuki

Published

on


Babban kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umurnin bayar da belin Sambo Dasuki tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a fannin tsaro”National Security Adbiser ( NSA)”.
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta bayar da belin ranar Litinin akan kuxi naira Miliyan 200 tare da masu tsaya masa guda 2.
Mai Shari’a Ojukwu ya zartar cewa, dole waxanda zasu tsaya masa su zama ma’akatan gwamnati masu matakin albashi na 16, su kuma mika wa magatakardar kotun takardar karin girman da aka yi musu na karshe a baki aiki.
Mai shari’ar ta kuma zartas cewa, in waxanda suka nemi tsaya masa ba ma’aikata gwamnati bane dole suma su bayar da jinginar naira Miliyan 100 wanda za a ajiye a asusun ajiyar bankin kotun. Maushari’ar ta kuma ce, dole waxanda zasu tsaya wa Dasukin ya zama sun mallaki kaddarori na filaye a yankin babban birnin tarayya su kuma ajiye takardar filayen a a kotu.
Ta kuma umurci a kotu ta ci gaba da rike takardar ‘passport’ na tafiye tafiye mallakin Dasuki.
A hukuncun nata, mai shari’ar ta ce, ci gaba da tsare Dasuki ba tare da an yanke masa hukunci ba karya dokan kasa ne, dokan da data ba shi ‘yanci ne a matsayinsa na xan Nijeriya kuma babu adalci a ci gaba da tsare shi.
A na tuhumar Dasuki ne da zargin karkatar da Dala Biliyan 2.1 a kotuna daban daban a yankin Abuja, ana kuma tuhmarsa da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba a wata kotun tarayya dake Abuja.


Advertisement
Click to comment

labarai