Connect with us

LABARAI

An Bukaci Manoma A Bauchi Su Rungumi Nomar Ridi

Published

on


An karfafa guiwar manoma a jihar Bauchi da su rungumi noman Ridi domin bunkasa tattalin arzikinsu.
Shugaban shirin bunkasa aikin noma na jihar Bauchi Dakta Iliyasu Aminu Gital shine ya bayar da wannan shawarin a lokacin kaddamar da shirin rarraba ridi hade da muhimman kayyakin gona da hukumar bunkasa aikin gona ra jihar Bauchi ta rabar, taron wadda aka kaddamar a karamar hukumar Giade.
Dakta Gital wanda ya bayyana cewar jihar Bauchi na daga cikin jahohin da suke matukar amfana da sanar noman Ridi, wanda ya bayyana nomar ta Ridi a matsayin noma mai cike da riba, don haka ne ya nemi manoma a jihar da su rungumi wannan fanninin domin tattalin arziki ya gabaka.
Shugaban wanda Daraktan malaman gona, Malam Musa Ahmad ya wakilceshi, ya bayyana cewar ma’aikatarsu za su ci gaba da tallafa wa manoman jihar da dabarbarun da suka dace domin kyautata sana’arsu ta noma.
Tun da farko kwamishinan ma’aikatar aikin gona na jihar Malam Yakubu Kirfi ya ce wannan yunkurin na daga cikin manufofin gwamnati mai ci na inganta aikin gona a fadin kasar nan.
Iri na ridi da yawansa ya kai buhu dubu daya ne aka raba a wannan yanking a manoma domin su rungumi wannan sashin.
Da yake jawabi a madadin wadanda suka amfana, shugaban manoman ridi kuma dakacin kauyen Dogowa Malam Aliyu Salihu ya yaba sosai da hakan hade da bukatar a fadada shirin.


Advertisement
Click to comment

labarai