Connect with us

LABARAI

2019: Hakeem Baba-Ahmed Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

Published

on


Hakeem Baba-Ahmed, daya daga cikin na hannun damar shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki, ya fice daga jama’iyyar APC.
Haka kuma Baba-Ahmed, wanda aka ba shi shugaban ma’aikatan Saraki a 2017, ya ce shawarar da ya yanke ba ta da alaka da shugaban majalisar.
“ Wannan takardar sanarwa an fitar da ita ne domin sanar da al’umma cewa na bar jam’iyyar APC. Na rubuta takarda rubutacciya zuwa ga shugaban jam’iyyar ta mazabata.
“Wannan wani mataki ne mai wahala, na barin jam’iyyar da na taimaka da gumina wurin kafuwarsa da nasarar lashe zabensa.
“Bayan shekaru uku da nasarar jam’iyyar, ina mai tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta gaza aiwatar da abin da a ke tsammani, wanda hakan ya sa na ga ba zai yiwu na iya ci gaba da zama membanta ba.


Advertisement
Click to comment

labarai