Connect with us

LABARAI

Za Mu Tabbatar Da Kyautata Tsaro A Filato, Inji ‘Safe Haben’

Published

on


Rundunar musamman ta Operation Safe Haben (OPSH) da ke karkashin rundunar soji ta baiwa mazauna Filato, Bauchi, da wasu yankunan Kudancin Kaduna tabbacin ci gaba da wanzar da tsaro da kare rayuka gami da dukiyar jama’a mazauna yankunan, hakan na zuwa ne biyo bayan samun kashe-kashen jama’a sama da 100 wasu sassan jihar Filato.
Da yake jawabi, jimkadan bayan wani atilsayen da suka gudanar wadda ya kunshi adadin jami’an rundunar da dama a cikin Jos da Bukuru, jami’in hulda da jama’a na rundunar OPSH Manjo Adam Umar, ya shaida cewar rundunarsu za ta tabbatar da sanya wa jama’a salama da aminci na kare rayukansu da dukiyarsu ba tare da wani taraddadi ba.
Ya shawarci jama’a da su yi kunnen uwar shegu da masu zanga-zanga suna yada karerayin da ka iya haifar da tashin-tashina, yana mai shaida cewa rundunarsu za ta ci gaba da sanya ido hade da tabbatar da kare rayukan jama’a a kowani lokaci.
Ya kuma shaida cewar za su narka jama’ansu a ciki da wajen mazauna domin dakile irin wadannan jita-jitan da ke tayar wa jama’a da hankula.
Ya ce, atisayen da rundunar Operation Safe Haben (OPSH) da hadin guiwar sauran bangarorin jami’an tsaro suka gudanar, sun yi ne domin su kara wa jama’a kwarin guiwa da kuma kara musu tabbacin cewar jami’ansu suna nan suna kokarin kawo karshen wani yananiya.
Umar ya kuma ci gaba da shaida cewar ba za su zura ido wasu tsiraru suna kokarin haifar da matsala da sunan addini ba, don haka ne ya shaida cewar sun samu karin jami’an daga shalkwatansu da ke Abuja, inda ya bayyana cewar kawo yanzu dukkanin shirye-shiryen ci gaba da baiwa jama’a kariya ya samu don haka ya nemi jama’a su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali, inda ya shaida musu kan cewar jami’an tsaro su ma suna gudanar da nasu aikin yadda y


Advertisement
Click to comment

labarai