Connect with us

LABARAI

’Yan Damfara Ke Gudanar Da Kanfanin Samar Wuta Na Discos, Inji ‘Yan Majalisar Wakilai

Published

on


A ranar Larabar da ta gabata ne babban kwamitin bincike na majalisar wakilai ta ce, kanfanin samar da wutan lantarki na “Nigeria Electricity Regulatory Commission (NERC)” da kuma kanfanin rarraba wuta na “Electricity distribution companies (Discos)” suna hada kai ne don danfara ‘yan Nijeriya ta hanyar dankara musu kudaden wutan lantarki masu yawan gaske.
Kwamitin da aka kafa don bincike da kawo karshen yadda kanfanonin ke karbar kudade masu dinbin yawa daga hannun ‘yan Nijeriya masu amfani da wutan lantarki, ta ce, bincikenta ya nuna cewar, yawancin ma’aikatan wadannan kanfanoni ‘yan danfara ne da suka shahara wajen cutar masu anfani da wutan lantarki a fadin tarayyar kasar nan
Kwamitin wadda Mista Israel Ajibola Famurewa dan jam’iyyar APC daga jihar Osun ke shugabanta, a zaman da suka gudanar a Abuja sun ce, kanfanonin NERC dana Discos sun gaza gaba daya wajen ganin jama’a sun mori kudaden da suke kashewa na wutan lantarkin da suke amfani da shi.
Da yake amsa tambayoyin ‘yan kwamitin, Shugaban kanfanin NERC, Farfesa James Momoh, ya ce, suna iyaka kokarinsu na ganin ana karbar kudin daya dace a hannun masu amfani da wutan lantaki da tare da an takurasu ba dai dai gwargwadon abin da suka yi amfani da shi.
Ya ce, a kan haka, kanfanin NERC ta taba karbar harajin Naira Miliyan 134.1 daga kanfanin Disco sabosa karya wasu kai’idoji, an kuma mika kudaden ga hukumar samar da wutal,lantarki ga karkara na “Rural Electrification Agency (REA)”
“Dukkan bayanan da kanfanin NERC keyi duk labarai ne kawai, abin da muke son sani shi ne hanyoyin da kuke shirin bi don kawo karshen wannan kudaden da ake karba a hannun mutanen dake amfani da wutan lantarki a kasar nan,” inji wani dan majalisar mai suna Raphael Nnanna dan jam’iyyar APC daga jihar Imo. Wani manban kwamitin mai suna Mista Muazu Lawal dan jam’iyyar APC daga jihar Zamfara, ya ce, “Daga dukkan alamu kanfanin Discos da masu ruwa da tsaki basu shirya yin wannan aikin ba.
“Kuma ci gaba da chazan kudaden a hanun mutane ba tare da la’akari da ainihin watan da suka yi amfani da shi ba, wannan abin na faruwa a dukkan fadin Nijeriya har da nan cikin Abuja. “Daga dukkan abin dake faruwa, ina tunanin ko dai ‘yan danfara ke gudanar da kanfanin Discos ko kuma sun shirya damfarar ‘yan Nijeriya kudade ne kawai, idan baku sjirya yin aikin ba ku gaya mana kawai.” Inji shi.
Shi kuwa, Mista Olayonu Tope, dan jam’iyyar APC daga jihar Kwara ya lura ne da cewa, “In da za a nemi ‘yan Nijeriya su jefa kuri’a game da yadda NERC ke gudanar da aiyyukanta dab a yadda za ta ci zabe don kuwa gada daya ta gaza a aiwatar da aiyukanta. Harkokin tattalin arzikin kasar nan ya ruguje ne saboda rashin wutan lantarki, wannan yana nuna cewar, NERC ce take jagorantar kasar nan zuwa halin tabarbarewar tattalin arzikin da ake fuskanta, tabbas lamarin NERC abin a yi tir da shi ne.
Haka kuma, dan majalisa Mista Solomon Maren dan jam’iyyar PDP daga jihar Filato, ya lura cewa, kanfanin NERC dana Discos sun hada baki suna ta damfarar mutane baji ba gani, hukumomi kuma sun zura ido basa komai akai.
“A garin Jos, kanfanin Discos na daura mita a kan palwaya, duk kudaden da mitan ya nuna sais u rarraba ga mutanen unguwan, mutane na biya kudaden wuta na abin da ya fi albashin da suke karba a wata..”
A nata gudunmawar, Misis Joan Mrakpor, ‘yan jam’iyyar PDP mai wakiltar jihar Delta, ta ce, wasu hanyoyin da kanfanonin wutan lantarkin ke amfani dasu wajen cutar jama’a sun hada da yanke wuta ga masu amfani da tsarin “Pay As You Go” tan a mai cewa, wanna lamarin baa bin da za a yarda da shi bane, “Dole ayi maganin wannan cutar da suke yi mana.”
A haddaiyar takardar da suka mika wa zaman kwamitin, Mista Azu Obiaya, shugaban kungiyar “Association of Nigerian Discos (ANAD)” ya ce, hanyoyin da kanfanonin samar da wutan lantarkin ke anfani dasu, hanyoyin ne na damfarar mutane kudadensu,musamman masu masa’anatu.
Ya ce, kanfanin Discos bata iya samar wa da ‘yan Nijeriya mita ba, saboda suna amfana da rashin haka wajen dorawa mutane kudade da sunan kudin wutan lantarki, kowa kumu ya san bah aka abin yake ba shekaru da suka wuce.
“Bamu iya ba jama’a mita bane saboda yawan jama’ar dake amfani da wutan lantarki, a halin yanzu bincike ya nuna cewa, a kwai masu amfani wutan lantarki fiye da Miliyan 3.5 da suke da mita yayin da wadanda basu da mita suka kai fiye da Miliyan 7.


Advertisement
Click to comment

labarai