Connect with us

LABARAI

Mutum Tara Sun Mutu A Hatsarin Babbar Hanyar Kaduna Zuwa Kano

Published

on


Mutum 10 ne suka rigamu gidan gaskiya a hatsarin daya auku a kan babban hanyar Kaduna zuwa Kano ranar Asabar.
Haka kuma mutum 9 ne suka mutu yayi da motoci fiye 54 kone kurmus yayin da tankar mai tayi bindiga a kan gadar Otedola dake babbar hanyar Legas zuwa Ibadan ranar Alhamis 28 ga watan Yuni.
Bayani ya nuna cewar hatsarin na hanyar Kaduna ya aiku ne kusa da makaratar Nuhu Bamalli Polytechnic” dake Zariya da misalii karfe 5:30 na safe.
A sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar FRSC ta yankin Zariya, Malam Idris yahaya ya fitar, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.
A cikin sanarwa, Mista Yahaya, ta ce, shugaban yankin Zariya na hukumar FRSC, Mista Muktar Zubairu, ya matukar gigiza da faruwar hatsarin.
“Hatsarin ya rutsa da motoci 3 ne, babbar motar daukan mutane mai lamba GDD 361 YE da wata karamar mota mai lamba SGR 57 DA sai kuma motar daukan kaya mai lamba LND 246 DE.
“Motocin guda uku ba daue ne da mutum 48, 9 daga cikinsu sun kone ne kurmus yayin da wata daga cikinsu ta rasu bayan an kai ta asibiti, mutum 31 kuma sun samau munanan raunuka, bayani ya kuma cewa, mutum 7 daga cikin wadanda hsarin ya rutsa dasu sun tsira ba tare da jin wani rauni ba.
“Direban babban motar daukan mutanen na kwance a asibitin koyarwa na ABU Shika.”
Shugaban FRSC na yankin Zariya ya ara da cewa, gaba dayan wadanda suka ji raunukan na kwance a asibitin ABUTH Shika, daga nan kuma ya yi kra ga dirrebobi masu yin doguwar tafiya dasu rinka nerman wuri suna tsatawa don mika kafa bayan sun danyi tafiya mai nisa.
“Yayin da direba ya yi tafiyar kamar na awanin 3 ko 4, ya kamata ya dan tsaya ya sauka ya mika kafarsa don baje gajiyar day a dauko, hakan zai taimaka wajen rage aukuwar hatsura a kan hanyoyinmu.
“Ya kamata kuma direbobi su rinka tuki da natsuwa musamman a cikin wannan lokaci na damina, su kuma tabbatar da suna amfani da sabbin tayoyin mota don kuma amfani da tsaffin tayoyi nada matukar hatsari.” Inji shi.


Advertisement
Click to comment

labarai