Connect with us

LABARAI

Labaran Bogi Ke Rura Wutar Rikicin Manoma da Makiyaya A Nijeriya –Binciken BBC

Published

on


Kafar watsa labarai na BBC ta bayyana cewa, labaran bogi na karya da ake watsa wa a kafafen sada zumunta na intanet yana taimaka wa wajen zafafa rikicin dake aukuwa a tsakanin makiyaya da manoma a fadin Nijeriya.
Rahoton ya kara bayyana cewa, “Labarai da hotunan karya na bogi wanda ake sanya da gangan ya yi matukar kara zafin rikicin dake tsakanin al’ummu a Nijeriya.”
Kafar watsa labaran dake watsa labaran ta a fadin duniya, ta bayar da misali da wasu hotuna dake yawo a kafafen sada zumunta na intanet inda ake yada cewa sun samo asali ne daga rikicin baya bayan ne daya auku a garin Jos ta jihar Filato.
“Wani mummunan hoto dake nuna wata mata a kwance a cikin jinni da wasu raunuka a jikinta, ana yawo das hi wai daga rikicin Jos yake.
“nan da nan aka yi ta watsa shit a kafar Twitter, amma abin mamaki wannnan hoton ya fara bayyana ne a kafar intanet tun a shekarar 2011, yayin da ake bayar da labarum cin zarafin mata a gidajen aure a Nijeriya, wani hoton ya kuma nuna mutane da yawan gaske da ake cewar wai sun mutu ne a rikicin da aka yi.
“Binciuke a kan hotunan ya nuna cewar lallai ba a Nieriya aka dauka ba, amma hoto ne da aka dauka na wani hatsarin motoci daya auku a shekarar 2015 a kasar Dominican Republic.
“Hotunan sun yi munin gaske, da kuma irin danyen maganganun dake biye da hotunan basu da dadi ko kadan.”
Kanfanin BBC ta kuma gano cewa, yada rahotannin da aba a tantance bad a gidajen watsa labarai na kasar nan keyi yana matukar taimaka wa wajen kara ruruta wutar rikicin tsakanin makiyaya da manoma a Nijeriya.
“A farkon wannan makon ne gidajen watsa labarai a Nijeriya da dama suka dauki wani labari dake cewar wai Malam Danladi Ciroma, wani shugaban kungiyar Miyetti Allah “Cattle Breeders Association,” ya ce, hare haren da aa kai jihar Filato wani ramuwar gayya ne na asarar shanaye 300 da suka yi.
Rahoton ta ce wai Ciroma ya ce,“Tun da bamu ga shanayenmu ba kada kowa ya tsammanin samun zama lafiya,
Mista Ciroma dai ya karyata wannan rahoton, kafar watsa labaran data yada rahoton kuma ta nemi ahuwa.


Advertisement
Click to comment

labarai