Connect with us

LABARAI

Kada Kuri’ar Kananan Yara A Jihar Kano: Hukumar Zabe Ta Fitar Da Sakamakon Bincike –Yakubu

Published

on


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce kwanan nan ne za ta bayyana sakamakon binciken da ta gudanar bisa zargin da aka yi na cewa, kananan yara da shekarunsu ba su kai na yin zabe ba, duk sun kada kuri’a a Jihar Kano.
Shugaban hukumar zaben, Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan ga editocin harkokin siyasa na gidajen yada labarai ranar Asabar a Legas.
Tun can baya, Shugaban ya bayyana a Abuja cewa, ko kusa hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano, ba ta yi amfani da rajstan zabenta ba a zaben kananan hukumomin da aka yi a Jihar.
Don haka sai ya ce, kamar yadda wasu masu ruwa da tsaki suka nema, kwanan nan hukumar ta kasa za ta bayyana sakamakon binciken da kwamitinta da ta kafa ya yi kan lamarin.
“Kwamitin da INEC ta kafa kan zargin, ya mika rahotonsa, har ma mun yi magana da manema labarai kan hakan, tabbataccen abu dai shi ne, ko kusa ba wata alaka tsakanin rajistan zabenmu da kuma abubuwan da suka faru na kada kuri’ar da yara kanana suka yi a Jihar ta Kano.
“Gaskiyan lamari ma shi ne, a rumfunan zabe da yawa, ba su ma yi amfani da wata rajistar tantance kowa ba.
Shugaban yana magana ne a wajen tantance sunayen da ke cikin rajistan, ya kuma ce, ya zuwa yanzun ba wani dan Nijeriyan da ya kawo mana kokensa kan mun saka wani da bai cancanta ba a cikin rajistan.
Sannan sai shugaban ya ce, a bisa hakan ma, hukumar za ta lika sunayen da ke cikin rajistan nata ko’ina a cikin kasarnan, za kuma ta baiwa dukkanin Jam’iyyun siyasar kasarnan kwafin rajistan domin su ma su tantance.
Yakubu ya ce, a lokacin da suka yi binciken a Jihar Kano sun baiwa manema labarai da kuma kungiyoyi rajistan domin su ma su tantance.
Ina son na ba ku tabbaci, za mu ci gaba da yin duk abin da ya dace domin kyautata inganci da sahihancin rajistan namu, musamman kan yadda muke kara kusantan babban zaben 2019.
Yakubu ya ce, daya daga cikin abin da hukumar na shi ta kirkiro shi ne, baiwa dukkanin masu kada kuri’a damar duba sunayensu a yanar gizo.
Da yake amsa tambaya kan zargin cewa, wai wasu jami’an hukumar na shi sukan nemi a ba su kudi kafin su yi wa mutum rajista, Yakubu ya ce, da yin rajistan da karban katin zaben duk a kyauta ne ake yin su.
Sai ya umurci ‘yan Nijeriya da su kai rahoton duk wanda ya nemi da a ba shi kudi a kan hakan.


Advertisement
Click to comment

labarai