Connect with us

LABARAI

Bacewar Miliyan 100: EFCC Za Ta Kai Ma’aikatan JAMB Biyar Kotu

Published

on


Hukumar EFCC ta shirya tsaf domin gurfanar da wasu jami’ai gaban kuliya, bisa zargin su da karkatar da kusan Naira milyan 100 na hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu, JAMB.
Daga cikin su akwai, Philomina Chieshe, ta ofishin hukumar ta JAMB da ke Makurdi, wacce ta yi ikirarin cewa wani markadeden maciji ya hadiye Naira milyan 36, daga cikin kudaden sayar da katin duba jarabawar hukumar da ake tarawa.
Cikin wadanda za a gurfanar din sun hada da, Mista Samuel Umoru, wanda a cewar Chieshe, shi ne ya umurce ta da ta karkatar da kudaden.
Sauran sun hada da, Tanko Labaran, ma’aikaci a ofishin hukumar ta JAMB da ke Jihar Nasarawa, wanda ya kasa biyan Naira milyan 23 na kudaden cinikin katin, da kuma jami’in da ke kula da ofishin hukumar a Kano, Yakubu Jakada, wanda shi ma ya zauna a kan Naira milyan 20 na kudin sayar da katin.
Su ma wasu jami’an hukumar ta JAMB da ke Gombe, duk za su gurfana gaban kuliyan.
Wata majiya ta hukumar EFCC din cewa ta yi, “Mun kammala duk wani bincike kan jami’an, kwanan nan ne kuma duk za mu gurfanar da su a gaban kotu.” Majiyar ta EFCC ta ce, Chieshe, wacce jami’a ce a ofishin hukumar da ke Makurdi, ta bayyana cewa, mai lura da ofishin hukumar na Makurdin ne yakan sanya ta ta ciro ma shi kudin sayar da katunan daga wasu asusun ajiyar hukumar da ke wasu bankuna biyu.
Majiyar ta ce, kafin a bullo da shirin asusun bai daya, jami’an hukumar ta JAMB, suna ajiye kudaden sayar da katunan ne a wasu asusun bankunan da ba a amince masu ba, wanda hakan ke sanya wa ana yin asarar bilyoyin naira.
Cikin bayanin da ta yi wa hukumar ta EFCC bayan ta yi rantsuwa, Chieshe cewa ta yi, “Ina karbo wadannan kudaden ne daga banki, wanda mai kula da ofishin namu yakan yi wasu ayyukan ofishin namu da su, a wasu lokutan kuma ya na yin amfani da kudaden ne domin amfanin kansa.”
Ta yi zargin cewa ta sha yi masa gargadi kan hakan, tana gaya masa cewa ba daidai ne ba, yadda yake kashe kudaden hukumar bisa gararin kansa, amma duk ba ya sauraron ta.
Wacce ake tuhuman, ta yi zargin cewa a kowane lokaci yakan nemi da a ba shi rance ne daga kudaden sayar da katin, amma ba ya dawowa da su.
Ministar kudi, Kemi Adeosun, ta ce a karo na farko, hukumar ta JAMB, ta zuba Naira bilyan 5 a asusun gwamnati, gami da alkawarin za ta sake zuba wasu Naira bilyan 3 a cikin asusun na gwamnatin tarayya, sabanin Naira milyan 3 da hukumar ta JAMB ke zubawa a kusan shekaru 40 a duk shekara.


Advertisement
Click to comment

labarai