Connect with us

LABARAI

An Yaba Wa Shugaba Buhari Game Da Kaddamar Da Aikin Gyaran Hanyar Kano Zuwa Abuja

Published

on


An bayyana cewa, lallai gwanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na bakin kokarinta wajen ganin harkokin sufuri da zirga zirga jama’a a kasar nan sun kara inganta, musamman idan aka kwatanta da shekarun baya, kamar yadda gwamnatin ta mayar da hankali domin samar da karin hanyoyi da kuma sababbi, domin kaucewa asarar rayuka da dukiyoyin al’uma da ake tafkawa saboda lallacewar hanyoyin kasar nan.
Wannan bayanan ya fito ne daga bakin babban manajan darakta na kanfanin A.I Global Oil and Transport, Alhaji Maharazu Ibrahim Adamu, a lokacin da yake tsokacin game sake sake kaddamar da gyara hanyar da ta taso daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya daga nan ta zarce zuwa Kano da gwamnatin tarayya tayi kwanakin baya, wanda babbban ministan ayyuka da gidaje Mista Babatunde Raji Fashola ya kaddamar a garin Ciromawa dake karamar hukumar Garunmalam a cikin jihar Kano.
Ga duk wanda ya san hanyan ya san ta yi matukar lallacewa musamman ramuka a bangarorin zuwa da dawowa wanda hakan ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin matafiya da masu motocin sufuri.
Malam Maharazu Ibrahim, ya ce, a matsayinsu na masu harkar sufuri sun fi kowa farin ciki da murna matukar aka kamala wannan aikin. ya yi imanin za a samu saukin asarar rayuka da dukiyoyin da kuma fashewar tayoyin motoci.
Sannan wani abin farin ciki inji Maharazu shi ne ba wannan hanya kadai gwamnatin ke aiwatar da gyaran hanyoyin ba kusan kasar gaba daya ake aiwatarwa .
Wuraren da masu manyan motoci suka fi samun matsala kamar garin Jaba, da Makwa suma yanzu sun zama tarihi. Sai ya jinjina wa shugaba kasar game da yadda kokarin kawo gyara da ci gaban al’ummar kasa.
Ya yi amfani da wannan dama da kira ga masu tuka manyan motocin daukar kaya da su guji tukin ganganci ko kuma guje guje marasa anfani a hanyar da zaran an kammala nan da shekaru uku masu zuwa, su kuma sanya tsoron Allah da kwatanta gaskiya .
Amatsayinsu na masu arkokin sufuri a shirye suke su ba da kudaden shiga watau tolget matukar gwamnati ta ce abayar. Masu kamfanonin sufurin motoci kuma su kara himmatuwa wajen tsabtace hakar sufuri, tare da taimakawa gwamnati ta fannonin da suka kamata musamman akan harka sufuri.
Daga karshe ya ce, harkokin sufuri a kasar nan na bayar da aikin yi ga al’umma musamman matasa da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnatoci, da fatan Allah ya kara bai wa jihar Kano da kasa baki daya zaman lafiya da karuwar arziki
Kaddamar da sake hanyar ya samu halartar gwamnonin Kaduna da Kano, da kuma sarakunan Kano dana Zariya da sauran manyar jami’an gwamnatin tarayya dana jihohin biyu da manya da kananan ‘yan siyasa.


Advertisement
Click to comment

labarai