Connect with us

LABARAI

Yadda Mu Ka Kwato Wa Jami’ar NOUN Yancinta –Farfesa Abdalla

Published

on


Idan ba a manta ba, a makon jiya mun tsaya da tattaunawar da Editan LEADERSHIP A YAU, NASIR S. GWANGWAZO, ya ke yi da mataimakin shugaban jami’ar NOUN mai cikakken iko, FARFESA ABDALLA UBA ADAMU, ne lokacin da farfesan ya ke yin bayani kan irin kalubalen da ya fuskanta a lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi a mukamin. A wannan makon Farfesa Adamu ya bayyana yadda ya shigo da tsarin dimukradiyya a nade-naden shugabannin tsangayunta da sassan jami’ar, inda kafin zuwansa nada su a ke yi, amma shi sai ya zo da tsarin gudanar da zabe. Ga yadda tattaunawar ta dora:
Wannan ba daidai ba ne; kamata ya yi a yi zabe. Na farko ma dai ban san mutane a nan ba, ballantana na ce wannan ka iya ko ba ka iya ba. Saboda haka a yi zabe. Kai da ka ke gurin, idan a ka bada sunanka a matsayin a zabe ka, idan ka iya su na son ka, sai su zabe ka. Idan ba ka yi ba kuma ba za su zabe ka ba. To, ka ga a ka yi wannan ma. Wadnnan na kadan daga cikin ’yan kalubalen da a ka fuskanta da kuma yadda a ka warware su. Amma kuma an samu hadin kai a jami’ar, saboda irin wadannan canje-canje da a ka kawo da kuma ba wa mutane fuska da kuma kyale mutane su shigo, don na ce kada wanda a ka hana shi ya zo ya gan ni. Ko waye ya ke son ya gan ni, ya zo ya gan ni ko malami ne ko ma’aikaci ne.

To, maganar sabon ‘portal’ da ka yi; a na maganar cewa ya na kawo wahalhalu wajen shiga yanar gizonku.
An ce da rarrafe yaro kan tashi. Lokacin da mu ka yi portal din nan sabuwa ta ke fil! Mun yi-mun yi su wadancan da su ka yi ma na na baya su ba mu manhajar, amma su ka ce ba za su bayar ba. Kai hatta lalitar dalibai, wacce idan yaro ya samu kudi zai je ya tara, sun hana, don akwai wadanda su ke yin wannan; da sun samu kudi sai su je su ajiye su na tarawa, don ba su san lokacin da za su sake samun kudin ba. To, hatta bayanan wadannan kudaden ya na wajen mutanen, sun hana mu. Saboda haka daga farko mu ka sake gina wata portal din. To, shi ne a ka samu matsaloli, saboda bayanan komai na hannunsu. Sai ka ga dalibi a shekara ta 2013 ya kamata a ce ya gama, amma bai gama ba. Kuma mun ce su ba mu bayanan sun hana mu. Sun ce wai saidai mu cigaba da tafiya tare su na rike ma na hannu, su na dan koya ma na. Mu ka ce ‘ba ma bukatar koyawarku, mu na da malamai kwararru, wadanda za su iya yin wannan abu. To, don me za mu saurare ku?’ Saboda haka kiran da zan yi ga duk wata makaranta shi ne, kada ta yarda ta kuskura a ce wai harkar bayananta (Data Management) ya na hannun wani kamfani. Ranar da duk ku ka samu sabani da kamfanin, to kullewa za su yi. Sai su mayar da ku wato kun zama yaransu, sai yadda su ka ga dama da ku, kuma su ce ba za su bude mu ku ba sai kun ba su wasu makudan kudi. To, amma idan ku ne ku ka zauna ku ka yi kayanku da kanku; da dadi babu dadi dai haka za ku mike. To, mu ma haka mu ka fara. Da farko a ka yi ta samun matsala… Kai a tsakaninmu ma sai da a ka samu matsala; wani bangaren ya na cewa wannan ba su iya ba, wani bangaren ya na cewa mu ne mu ka iya. To, duk sai da na zauna na daidaita sahun kowa da kowa, sannan mu ka samu inda za a rike ma na portel din a yanar gizo, saboda da yawansu ba a Najeriya a ke yin su ba. Saboda haka wajen 2016 har wajen tsakiyar 2017 gaskiya an samu wadannan matsalolin, amma kuma daga wajen Agusta abinda ya yo sama abin ya riga ya dawo daidai; yanzu babu wanda ya ke yi ma na maganar korafi ya ce da mu wai ya kasa shiga ko wani abu makamanci. A na yi ma na maganar sakamakon jarrabawa ya makale, amma irin wadannan matsaloli duk burbushin irin wadancan mutanen ne, kuma mu na nan mu na ta kokarin yadda za mu warware matsalar.

To, kenan yanzu duk wani bayanan dalibai ya samu?
Kwarai da gaske. Abinda na ke so na gaya ma shi ne, idan dai ka na neman wani bayani na dalibi a take a wajen da ka danna zai ba ka bayani. Amma kuwa da a lokacin da mu ke a hannun wadancan mutanen babu yadda za mu samu haka, sai abinda su ka ga dama su ka ba mu. Misali, idan mu na so mata nawa ne su ka yi rijista da NOUN a Kano, ba za su iya gaya ma na ba, amma yanzu mu na iya samun abin da kanmu.

Bayan zuwanka ko ka kirkiro sababbin kwasa-kwasai a jami’ar nan ta NOUN?
Akwai guda biyu da mu ka kirkira, amma ragowar ba sababbi ba ne. Lokacin da na zo sai na tarar cewa hukumar tace kwasa-kwasai ta jami’o’in Najeriya, wato NUC, ta na yi ma na wani kallon hadarin kaji, saboda su na ta gurnanin mu na yin kwasa-kwasai ba tare da sahalewarsu ba. Sai na ce a tattaro duk kwasa-kwasan da mu ke da su, sai mu ka cewa NUC ga kwasa-kwasan da na zo na tarar a na koyarwa a jami’ar nan, ku na min wadanne ne ku ka san da su wadanne ne ba ku san da su ba. Wato su ware wadanda su ka amince da su kuma bayan shekara biyu su ka dawo su ka tantance yadda a ke tafiyar da su, kamar yadda tsarin ya tabadar. Sai da su ka cire kwasa-kwasai 39 su ka ce ba su san da su ba. Sai na ce to tunda ba ku san su ba, mun zabge su.

To, ya a ka yi da daliban da su ke daukar kwasa-kwasan?
Sai su ka ce da mu daliban da su ka shiga wadannan kwasa-kwasan ku kyale su su gama, saboda mun ce idan mu ka ce mun kori daliban alhali sun biya kudi da sauransu, za su kai mu kara. Saboda haka don gudun kada wata husuma ta tashi abinda za ku yi ma na shi ne, ku kyale mu mu yaye su a matsayin cewa wannan digirin an daina yin sa, amma dai ka na da shi. To, sai su ka kyale mu. To, a haka mu ke. Kwas din Law sun yarda da shi, to amma saboda matsalar da dalibanmu su ke fuskanta wajen shiga Law School (makarantar zama kwararren lauya), saboda Legal Council of Education (majalisar kula da ilimin lauyoyi) sun ce ba su yarda dalibanmu su shiga ba, sai mu ka ce mun dakatar da shi. Wannan tun ma kafin na zo ne. To, kokarin da mu ke yi shi ne mu yi kwas din digiri na biyu da digirin digirgir (PhD) a Law din yadda duk daga inda ka ke ko namu ne ko wani wajen ne digirinka, sai ka zo ka yi. Wato mu na so mu rage karfin shi digirin farko har sai an warware waccan takaddama. To, ka ji yadda a ka yi.

A makon gobe za mu ji matsayin zuwa hidimar kasa (NYSC) da digirin jami’ar NOUN. A tara in sha Allahu.


Advertisement
Click to comment

labarai