Connect with us

LABARAI

NSCDC Ta Ba Wa Jami’ai 550 Horo Don Yaki Da ‘Yan Ta’adda A Zamfara

Published

on


Hukumar tsaron farin kaya, wato Nigeria Security and Cibil Defence Corps, ta bi sahun rundunonin tsaro na kasar nan don kawo karshe ‘yan ta’addan da su ka addabi jihar Zamfara, inda hukumar ta bai wa jami’anta 550 horo. Kwamandan hukumar, D.A. Abi ne ya bayyana haka a lokacin yaye dakarun da su ka samu horon a Gusau baban birin jihar Zamfara.
Kwamanda Abi ya kuma bayyana cewa, wannan horon ya samu amincewar babban kwamanda na sojojin kasa wanda ya ba su sojoji da su ka horar da jami’an rundunar tasu na tsawon wata uku, ya na mai kara wa da cewa, “kuma yanzu haka mun samu mutane 550 da su ka samu wannan horon na sarrafa bindiga da kuma dabarun yakin ‘’yan ta’adda.
“Sakamakon samun wannan hotarwa jami’an namu ba su shakar shiga ko’ina don fatatakar ’yan ta’adda da Sara-Suka da barayin shanu a fadin jihar ta Zamfara.”
Kwamandan ya yi kira ga shugabanin kanaan hukumomi da gyara wa rundun ofisoshinsu don samun damar inda za su ajiye wadannan makamai domin tunkarar ‘yan ta’adda.
A karshe Kwamandan ya mika godiyar sa ga shugaban rundunar sojoji Birgediya Janar L. M. mai kula da bataliya ta 223 da ke Gusau, wanda ya ba su masu horar da su da kuma Gwamna Abdula’aziz Yari Abubakar da ya dauki nauyin tafiyar da wannan horon da kuma ko’odineta na hukumar kula da hidimar ksa, NYSC, wacce a ka yi amfani da wajensu wajen gudanar da wannan horo.
A nasa jawabin Shugaban NSCDC na kasa, Kwamanda Janar Abdullahi Gana Muhammad, ya bayyana jin dadinsa da a kan horar da wadannan dakaru, ya kuma bayyana cewa rundunarsa ta shirya tsaf don ganin sun fatatakin ‘yan ta’addan da su ka addabi jihar Zamfara da kasa bakidaya, kuma wannan horon da rundunar ta samu na daga cikin kwarin gwiwa da gwamnatin tarayya ke ba su a kodayaushe.
Shi ma a nasa jawabin shugaban bataliya ta 223 da ke Gusau, Birgediya Janar L.M. ya bayyana cewa, a shirye su ke a koda yaushe don bada horo, kuma su yi aiki tare, domin wadanda su ka samu wannan horon lallai za su taimaka wajen samar da tsaro a jihar.
Shi ma a nasa jawabin Gwamna Abdula’aziz Yari da ya samu wakilcin mataimakinsa, Malam Ibrahim Wakkala Liman, ya bayyana cewa, gwamnatin jihar na iyaka kokarinta wajen taimakon jami’an tsaro. Don haka yanzu ta ba wa wannan rundunar fili don gina ma ta babbar hedikwata a cikin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara. Ya kuma ce, kofarta a bude ta ke wajen amsar shawarwari da kuma taimaka wa hukumomin tsaro.


Advertisement
Click to comment

labarai