Connect with us

LABARAI

Kotu Na Neman Manoman Alkama 1,974 Ruwa A Jallo A Kano

Published

on


Yanzu haka wata kotun Majestiri da ke Kano ta bada umarnin kamo wasu Manoman Alkama su 1,974 da suka gaza biyan bashin da aka basu na Noman Alkama a shekarar da ta gabata Manoman Alkama da kimanin 2000 ne suke cikin tsaka mai wuya sakamakon taurine bashi da suka gaza biya bayan an basu makudan kudade dan gabatar da Noman Alkama da Hukumomin bunkasa aikin Noma na Kasa da goyan bayan Gwamantin Jahar Kano.
Wannan bayanin ya fitone daga bakin Alhaji Rabi’u Faruku Mudi shugaban kungiyar Manoma ta Kasa AFAN kuma shugaban kungiyar masu Noman Alkama ta kasa reshen Jahar Kano cikin wata hira da yayi Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN kamar yadda muka samu daga majiyar mu ya ce cikin Manoman Alkama 2000 da suke cikin matsala a yanzu sakamakon taurine bashi daga Manoman yanzu haka an gabatar da 26 a gaban Kotu yayin da kuma Kotu umarci a damko sauran Manoman Alkama 1,974 domin gurfanar dasu a gaban Kotu.
Sai dai kuma wakilin mu yayi nazari akan yadda Manoman Alkama da aka ba bashi suka fuskanci kalu bale dan gane da yadda farashin Alkama ya karye wan war a dai shekarar da ta gabata kafin wannan lokaci Buhun Alkama na kai kimanin 40,000 wanda kuma a yanzu haka ya ke kasa da 20,000 idan kayi la’akari da yadda kwanan Alkama baya wuce 450 zuwa 500 kamar yadda wakilinmu yayi bincike akan lamarin.
Haka kuma an ruwaito manya manyan Manoman Alkama na kiraye kiraye da Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jahohi akan su taimaka su bullu da tsarin saye Alkamar da Manoma suka Noma aka barsu da ita wanda mafiya yawa kudin da suka kashe wajan Noma Alkamar Alkamar bata mai da kudin ta a kasuwa sakamakon karyewar farashi da Alkamar tayi idan akayi la’akari da yadda farashinta yake a loakcin shukata da kuma yadda farashinta yake a yanzu bayan an girbeta dan haka akwai bukatar Gwamnati ta kawo dauki dan bunkasa noman Alkamar mai makon durkushewar Nomanta da ka’iya faruwa muddin Gwamnati bata dau matakin ba Hausawa dai na cewa ba ayiwa Manomi dariya in bai siyarba ya cinye kayarsa.


Advertisement
Click to comment

labarai